kamus
Hausa Dictionary
Translation | Koyon Turanci |Quran Search




1. Shin kalmomi nawane a cikin wannan ƙamus ɗin yansu?

Babu wata kalmar turanci ko kalmar hausar da bamu sanya a cikin wannan ƙamus ɗin ba in banda wasu 'yan kaɗan kodai saboda mun kasa fassara su ko kuma saboda rashin muhimmancin su da muke gani. Bamu tsaya a sanya kalmomi kawai ba, kusan kowace kalma mukan kawo misalanta a cikin jimla domin mutane susan yanda ake anfani da kalmar.

2. To amma me yasa sauda yawa idan na bincika ban samun wasu kalmomi a ciki?

Idan aka bincika ba tare da samun sakamako ba to adai duba da kyau ko anyi kuskuren rubuta kalmar da ake bincike, kuma sannan ka tabbata kana yin amfani da haruffan Hausa masu lanƙwasa a gurin daya kamata ayi amfani dasu. Idan wayarka bata ɗauke da haruffan Hausa to ka shiga play store kayi install wannan app mai suna Switch Keyboard a wayarka wanda zai baka damar yin amfani da haruffan Hausa dama na turanci. Idan kuma har kalmar dai dai ce, to

Yana da kyau a lura da cewa:

  1. Bamu sanya kalmomin 'plural' waɗanda ake samad da su ta hanyar sanya 's' ko 'es' a ƙarshen kalma
  2. Galibi bamu sanya kalmomi masu ɗauke da 'past participle' (waɗanda ake sanya musu 'ed' ko 'd' a ƙarshensu)
  3. galibi bama sanya kalmomi masu ɗauke da 'present perticiple' wato kalmomin da ake samar dasu ta hanyar sanya haruffan 'ing' a ƙarshen kalma. Misali kalmar 'going' wacce aka samad da ita daga cikin kalmar 'go'
  4. Bamu sanya 'comparative' da kuma 'superlatives' na 'adjectives' (misali 'low' {ƙaranci}, lower {matsakaici} sai kuma 'lowest' (mafi ƙaranci) mukan sanya 'Adjectives' ɗin ne kawai, wato 'low'
  5. akwai waɗansu kalmomi waɗanda suke ɗauke da 'prefix' ko kuma 'suffix' waɗanda muka tsallake bamu sanyasu a cikin wannan ƙamus ɗin ba
  6. Don haka yana da muhimmanci ku duba waɗannan shafukan na ƙasa domin sanin yanda kalmomi ke canzawa, don kuwa ina ganin muddin mutum ya gane asalin kalma to zai iya gane ma'anan dangoginta
Singular And Plural

Prefix And Suffix

Tenses

Parts of Speech

Muddin mutum ya gane asalin kalma to zai iya gane ma'anar dangogin ta, misali kalmar 'appreciate' ana fidda kalmomi har bakwai daga cikinta kamar haka: 'appreciates, appreciator, appreciatory, appreciable, appreciation, appreciative, appreciating,' sannan kuma bayan an fidda waɗannan kalmomin bakwai, suma haka za a iya fidda wasu kalmomin daga cikinsu kamar haka: 'appreciatively, appreciativeness, appreciable, appreciably, appreciatingly' to idan kun duba zaku ga kalma ɗayace 'appreciate' amma ta zama goma sha biyu. idan mutum baida masaniya akan darasin 'suffix' zai iya tunanin cewa ko waɗannan wasu kalmomine mabanbanta, amma a zahiri waɗannan kalmomin goma sha biyu duk suna ɗaukan kusan ma'ana guda ne. Kaman dai a hausa ne kalmar 'aiki' akan fidda kalmomi har goma sha huɗu daga cikinta kamar haka: 'ayyuka, aika aika, ma'aiki, ma'aikiya, ma'aikaci, ma'aikaciya, ma'aikata, (gurin aiki), ma'aikata (masu aiki), ma'aikatu, ma'aika, aikace, aikatau, aikatu, aikatuwa'. To kaman hakane misalin kalmomin turanci masu ɗauke da 'suffix' yake, muddin kuka gane haruffan da ake anfani dasu gurin canza kalma to bakwa buƙatan neman bincika ma'anan kalmomi masu ɗauke da 'suffix'. Domin koyon wannan darasin sai ku duba gurin 'prefix and suffix'

3. Me yasa wasu lokutan idan na bincika kalma na ke samun fassarar da ta banbanta da wacce na samu a wasu ƙamus ɗin?

Muna yin anfani da Longman Dictionary da kuma oxford dictionary ne wajen zaƙulo kalmomin da daga bisani muke fassara su zuwa hausa. A zahiri a wasu lokutan akan samu saɓanin fassara tsakanin wasu "dictionaries" ɗin. Kuma sannan waɗansu kalmomin na ɗaukan ma'anoni daban dabam. Domin neman ƙarin bayani duba shafin homonyms

4. Me yasa nake ganin kalmomi da yawa kuna yi musu fassara iri guda?

e, turanci yana da wannan, domin neman ƙarin bayani duba shafin synonyms

5. Me kuke nufi da "idan akai anfani da kalmar a lokacin da ya wuce"?

muna nufin kalmar ko dai "past tense" ce ko "past perfect tense" don neman ƙarin bayani duba shafin tenses

6. Na samu wasu kalmomin da kuka rubutasu ba yanda ya kamata ba, ko kuka fassara su da fassarar da ba shine ya dace da su ba.

muna maraba da shawarwari ko kuma gyara idan an samu kuskure a cikin wannan ƙamus ɗin ko ma dai sashin koyon turanci na wannan website. Zaku iya tuntubanmu ta nan


English Hausa Dictionary/Kamus

English to Hausa Words list

A-B-C-D-E-F-G-H-I-J-K-L-M-N-O-P-Q-R-S-T-U-V-W-X-Y-Z

Hausa to English Words list

A-B-Ɓ-C-D-Ɗ-E-F-G-H-I-J-K-Ƙ-L-M-N-O-R-S-T-U-W-Y-'Y-Z

Kamus.com.ng is an online/offline English to Hausa And Hausa to English comprehensive bilingual Dictionary (or Kamus in Hausa) containing thousands of British and American English words/phrases and Abbreviations.

The website/app provide definition of any existing English or Hausa word and phrase.

Each words came along with parts of speech.

We included hausa descriptions of complex and ambiguous definitions

We specified British Audio and IPA pronunciation of any English word for those wishing to know how to pronounce a particular word.

We provide English & Hausa bilingual usage sentences, description images, audio pronunciations of all Hausa words, pluralization of Hausa words, and origins of Hausa words derived from Arabic or English.

However this website came along with English to Hausa learning resources designed specifically for native Hausa wishing to learn English as second language.

Scientific words, medical words, geology, geography, biology, anatomy, chemistry, physics, literature, computing, psychology and linguistics words were included and precisely translated to Hausa.

Enjoy your stay here and also contribute to its growth by linking to us or inform others about this website.

The dictionary is frequently being updated and it works both online and offline.

If there is any missing word in the dictionary please send us the word and we'll add the word as soon as possible

Aika Zuwa

Whatsapp

Copyright © 2014-2024 kamus.com.ng. All rights reserved