Singular And Plural


Download this Video

Singular is referring to just one person or thing. while plural denoting to more than one person or thing


"Singular" yana nufin abu guda ɗaya, sannan kuma "Plural" yana nufin abubuwa masu yawa (= jam'i)

Plural noun is mostly made by adding "s" to the end of a word. e.g


Galibi ana samar da "plural" ne ta hanyar sanya "s" a ƙarshen kalma. Misali:
Singular (Tilo)Plural (Jam'i)
Boy (yaro)boys (yara)
girl (yarinya)girls ('yanmata)
book (littafi)books (littafai)
cat (mage)cats (maguna)
weeks (mako/sati)weeks (makwanni)

But if the final letter of the noun is "ch", "s", "se", "sh", "x", or "o", the plural can be formed by adding "es", for example:

Amma idan harafin ƙarke na kalma ya ƙare da waɗannan haruffan "ch", "s", "se", "sh", "x" ko "o", to akan samar da plural ne ta hanyar sanya "es" a ƙarken kalma.
Misali:


SingularPlural
Brush (buroshi)brushes (buroshi fiye da ɗaya)
box (akwati)boxes (akwatuna)
potato (dankali)potatoes (dankali da yawa)
horse (doki)horses (dawakai)
gas (iskar gas)gases (gas da yawa)
torch (cocila)torches (cociloli)
watch (agogo)watches (agogo da yawa)
dress (suturar mata)dresses (suturun mata)

If noun has 'y' as its final letter, the 'y' is usually change to 'i', then 'es' should be added to the word thereafter to form plural.


Idan harafin "y" shine harafin ƙarke na kalma, to anan akan samar da jam'in wannan kalmar ce ta hanyar canza "y" ya zama "i", sannan daga bisani a sanya haruffan "es".
Misali:
Singular (tilo)Plural (jam'i)
lady (mace)ladies (mata)
baby (jariri)babies (jarirai)
army (rundunar soji)armies (rundunar sojoji)
city (birni)cities (birane)
body (jiki)bodies (jikuna)

Plural can be formed by changing "f" to "v", then "es" to be added afterwards. E.g.Za'a iya samar da "plural" ta hanyar canza "f" ya koma "v" sannan a sanya haruffan "es" a ƙarshe.
Misali
.
Singular (tilo)Plural (jam'i)
leaf (ganye)leaves (ganyayyaki)
life (rai/rayuwa)lives (rayuka)
self (kai)selves (su)

But some nouns are different in plural form


To amma waɗansu kalmomin yanayin yanda ake jam'insu ya banbanta.
Misali
Singular (tilo)Plural (jam'i)
Man (namiji)men (maza)
mouse (ɓera)mice (ɓeraye)
oasis (gurin yada zango)oases (guraren yada zango)
goose (ƙwaƙwa)geese (ƙwaƙwa da yawa)
tooth (haƙori)teeth (haƙora)
woman (mace)women (mata)
foot (tafin ƙafa)feet (tafin ƙafafu)
ox (sa wanda aka dandatse)oxen (shanu waɗanda aka dandatse
child (yaro ko yarinya)children (yara)

Some words don't change in plural.


Waɗansu kalmomin kuwa yanayin yanda ake rubuta tilon su da kuma jam'in su duk yanayi guda ne.
Misali:
Singular (tilo)Plural (jam'i)
sheep (tinkiya)sheep (timakai)
swine (alade)swine (aladu)
deer (barewa)deer (barewa da yawa)
trout (kalfashe)trout (kalfasai)
salmon (kifin teku)salmon (kifayen teku)
cod (babban kifin teku)cod (manyan kifayen teku)
cannon (makamin yaƙi)cannon (makaman yaƙi)
dozen (goma sha biyu)dozen (jam'in 'dozen')
gross (kuɗi)gross (kuɗaɗe)

Some words have two plural forms.


Waɗansu kalmomin suna da yanayi biyu na yanda ake jam'insu.
Misali:
Singular (tilo)Plural (jam'i)Plural 2
penny (sile)pennies (silalla)pence (silalla)
pea (waken fis)peas (jam'in 'pea')pease (jam'in 'pea')
genius (ɗan baiwa)genuises ('yan baiwa)genii ('yan baiwa)
brother (ɗan uwa)brothers ('yan uwa)brethren ('yan uwa)
person (mutum)persons (mutane)people (mutane)

Some words have no plural. E.g.


Waɗansu kalmomin basu da jam'i, misali:

advice (shawara), information (bayanai), knowledge (ilimi), news (labarai), progress (mataki, wakana), work (aikin da mutum yake yi a matsayin sana'a) money (kuɗi), luggage (jakunkunan matafiya), furniture (kayan ɗaki), scenery (siffar guri), machinery (mashina)

Aika Zuwa

Whatsapp

Home

© Copyright. Shamsuddeen Zakariya. All right reserved.