meaning of use in Hausa | Hausa Dictionary | English Hausa Dictionary
kamus
Hausa Dictionary
Our App | Koyon Turanci |Quran Search






Definition of use in Hausa

use

verb & noun /juːz/
1. Amfani da
2. Laƙume, cinye, shanye
3. Yiwa mutum wayo
4. Ci da gumin wani
5. Yin amfani da wata dama domin amfanar da kanka
6. Use to: kasancewa
7. Amfanin abu
8. Amfani
9. Make use of something: yin amfani da abun daya samu
10. The use of something: damar yin amfani da abu
11. Laƙumewa

Example of use in a sentence

  1. Amfani da
  2. Verb

    I need an empty soft drink bottle that has been used. ina buƙatar kwalbar lemun da aka yi amfani da ita.

    Why do you want to use soft drink bottle? me yasa kake son yin amfani da kwalbar lemu?

    I will use all my money for buying computer. zanyi amfani da ilahirin kuɗaɗena gurin siyan kwanfuta.

    He bought a car that he abandoned later and never used any more. ya siya motar da yayi watsi da ita ba tare da yana yin amfani da ita ba.

    Soap are used for bath and washing clothes. ana yin amfani da sabulu ne domin wanka da kuma wanke tufafi.

    There is no need to use force against them if they lay down their arms. babu buƙatar ayi amfani da ƙarfi a murƙushe su idan suka ajiye makamansu.

    He uses abusive expression if he's angry. yana yin amfani da kalamai na zagi idan yayi fushi.

  3. Laƙume
  4. How comes he used up such large amount of money within one week? ta yaya aka yi ya cinye irin wannan kuɗin mai yawa a cikin mako guda?

    His parents are going to send him more money when he use up his foods. iyayensa zasu aiko masa da ƙarin kuɗi idan ya gama cinye abincinsa.

  5. Yiwa mutum wayo, ci da gumin wani, yin amfani da wata dama domin amfanar da kanka
  6. She dumped her boyfriend when she realized he's just using her. ta fita a harkar saurayinta bayan data fahimci cewa yana yi mata wayo ne kawai.

    He is just using this situation to attract people to his website. kawai yana yin amfani da wannan yanayin da ake ciki ne domin jan hankalin mutane zuwa ga shafinsa na internet.

    The shop owner use her because she is so beautiful. mai shagon yana yin amfani da ita ne domin samun ciniki saboda ita kyakkyawa ce.

    The illegal immigrants are being used and abused by the natives. 'yan ƙasar suna ci da gumin baƙin hauren kuma suna cutar dasu.

  7. Kasance
  8. Where did he use to go? ina yake zuwa?

    We didn't use to stay at home in the morning. bamu kasance muna tsayawa a gida ba da safiya.

    Noun

  9. Amfani
  10. Crude oil is a multipurpose fuel that has a variety of uses. ɗanyen man fetir mai ne da ake yin amfani dashi domin yin abubuwa mabambanta.

    He bought an expensive car but abandoned it later because he didn't find a use for it. ya sayo mota mai tsada amma ya daina aiki da ita saboda amfaninta ya ƙare.

    That's the reasons why I can't buy a car because I don't have any use for one. hakan shi yasa bazan iya siyan mota ba saboda banga amfaninta ba a gareni.

    I'm happy that you put your money and time into good use. nayi farin-ciki daka kake yin amfani da kuɗaɗenka da lokacinka a hanyar data dace.

    The computer is going to corrupt the audio if you interrupted it when it's in use. kwanfutar zata lalata sautin muryar idan har ka dakatar da ita lokacin da ake aiki da ita.

    Children can break that car when it is not in use for a while. yara zasu iya lalata motar nan idan aka jima ba'a yin amfani da ita.

    This kind of bottle is now out of use. a halin yanzu ba'a yin amfani da irin wannan kwalbar.

    We don't observe any decrease in the use of Hausa language in Nigeria. bamu ga alamar raguwar yin amfani da harshen Hausa ba a Nigeria.

    They make use of their youth. suna cin moriyar ƙuruciyarsu.

    What's the uses of crude oil? me ake yi da ɗanyen man fetir.

  11. Damar yin amfani da abu
  12. My wife have the use of my bank account. matata tana da damar yin amfani da asusun ajiyana na banki.

    If you have a stroke you can lost the use of your arms or legs voluntarily. idan kana fama da cutar bugun jini zaka gaza iya yin amfani da hannayenka ko ƙafafuwanka.

  13. Laƙumewa
  14. He can bath and dress up without the use of cream in hot season. zaka iya yin wanka da canza kaya ba tare da shafa mai ba a lokacin zafi.

Probably Related words: cause, because, excuse, house, louse, museum, pause, refuse, trousers, useful

Nearest words:
used, user, use to, useful, used to, useless, username, usefulness, user-friendly,


English Hausa Dictionary/Kamus

English to Hausa Words list

A-B-C-D-E-F-G-H-I-J-K-L-M-N-O-P-Q-R-S-T-U-V-W-X-Y-Z

Hausa to English Words list

A-B-Ɓ-C-D-Ɗ-E-F-G-H-I-J-K-Ƙ-L-M-N-O-R-S-T-U-W-Y-'Y-Z

Kamus.com.ng is an online/offline English to Hausa And Hausa to English comprehensive bilingual Dictionary (or Kamus in Hausa) containing thousands of British and American English words/phrases and Abbreviations.

The website/app provide definition of any existing English or Hausa word and phrase.

Each words came along with parts of speech.

We included hausa descriptions of complex and ambiguous definitions

We specified British Audio and IPA pronunciation of any English word for those wishing to know how to pronounce a particular word.

We provide English & Hausa bilingual usage sentences, description images, audio pronunciations of all Hausa words, pluralization of Hausa words, and origins of Hausa words derived from Arabic or English.

However this website came along with English to Hausa learning resources designed specifically for native Hausa wishing to learn English as second language.

Scientific words, medical words, geology, geography, biology, anatomy, chemistry, physics, literature, computing, psychology and linguistics words were included and precisely translated to Hausa.

Enjoy your stay here and also contribute to its growth by linking to us or inform others about this website.

The dictionary is frequently being updated and it works both online and offline.

If there is any missing word in the dictionary please send us the word and we'll add the word as soon as possible

Aika Zuwa

Whatsapp

Copyright © 2014-2024 kamus.com.ng. All rights reserved