meaning of take in Hausa | Hausa Dictionary | English Hausa Dictionary
kamus
Hausa Dictionary
Our App | Koyon Turanci |Quran Search


Definition of take in Hausa

take

verb /teɪk/
1. Ɗauka, ɗauko, ɗauki, ɗauke
2. Cire, zare
3. Ɗaukan abu zuwa wani guri
4. Karɓa
5. Ɗauka cewa
6. Riƙe
7. Zuwa wani guri tare da wani
8. Tafiya akan abun hawa
9. Tafiya akan wata hanya
10. Buƙatar
11. Ɗaukan tsawon lokaci
12. Shan magani ko ƙwaya
13. Yiwa lamari wata iriyar fahimta
14. Matsayin mutum akan abu
15. Yin bazata
16. Karɓe
17. Ra'ayin mutum game da abu
18. Take someone by surprise: yiwa mutum ba-zata
19. Take on something: ra'ayin mutum akan abu
20. Take a: aikata wani abu

Example of take in a sentence

 1. Ɗauke
 2. Remember to take the chair when you go. ka tuna ka ɗauko kujerar idan ka je.

  They took the patient to hospital in a car. sun ɗauki mara lafiyan zuwa asibiti a mota.

  Take the car to the garage to be repaired. ɗauki motar zuwa gurin gyara motoci domin a gyarata.

  Her purse had been taken from her. an ɗauke mata jakarta.

 3. Cire, zare
 4. Five thousand naira will remain if you take away three thousand naira from the money. naira dubu biyar zai rage idan ka ciri naira dubu uku daga cikin kuɗin.

 5. Ɗaukan abu zuwa wani guri
 6. Make sure to take your ATM card to the bank. ka tabbatar da cewa ka tafi da katinka na zarar kuɗi idan zaka tafi banki.

  The phone he purchased online were taken to his hometown in Kano. an kai masa wayar daya saya zuwa garinsu dake Kano.

  Please take this baby down to his mother. ɗan kai wannan yaron zuwa ga mahaifiyarsa.

 7. Karɓa
 8. I need a restaurant that take credit cards because cash is scarce. ina buƙatar gidan siyar da abinci dake karɓar katin ATM domin takaddun kuɗi sun yi wahala.

  My brother doesn't take milk because he has an allergic reaction to it. ɗan uwana baya shan madara saboda cikinsa baya iya narkar da ita.

  An average ATM machine will take millions of Naira. na'urar zarar kuɗi guda ɗaya takan ɗauki miliyoyin kuɗaɗe.

  I can't take all this kind of mistreatment. bazan lamunci irin waɗannan wulaƙancin ba.

  That's really a good idea - I take your point. lalle wannan shawara ce mai kyau - na amince da maganarka.

  It left for you either to take it or not. shawara ta rage gareka ko dai ka amince ko kada ka amince.

 9. Ɗauka cewa
 10. Hausa are taken to be originated from Ethiopia by some historians. wasu masana tarihi sun ɗauka cewa Hausawa daga Habasha suka samo asali.

  Ethiopians and Hausas don't look alike and there's no way we could have taken them as the same tribe. mutanen Habasha da Hausawa basa kama da juna don haka babu yadda za'a yi mu ɗauka cewa su ɗin ƙabila guda ce.

  What do you take Hausa for? Hausa are black but Ethiopians are not. me kake ɗaukan Hausawa ne? Hausawa baƙar fata ne amma mutanen Habasha su ba baƙaƙe bane.

 11. Riƙe
 12. She asked her husband to take the baby while she enters the bus. ta buƙaci mijinta daya riƙe yaron a daidai lokacin da take shiga motar.

  You will definitely get a lot of stares if you take your girlfriend hands passing through a crowd. lalle zaka sha kallo idan ka wuce ta cikin jama'a kana mai riƙe da hannun budurwarka.

  Ask her to take hold of the kettle. kace da ita ta riƙe butar.

 13. Zuwa wani guri tare da wani
 14. We take our children to resort every weekend. muna kai yaranmu gurin shaƙatawa duk ƙarken mako.

  I'm going to take my girlfriend to my parents house. zan kai budurwata gidan iyayena.

 15. Tafiya akan abun hawa, tafiya akan wata hanya
 16. Many people now prefer to take a train. mutane da dama yanzu sunfi son shiga jirgin ƙasa.

  Who are those going to take the Lagos to Kano flight? su waye waɗanda zasu hau jirgin Legas zuwa Kano?

  The bank is far away from the town but you can get there earlier if you take the Tudun wada road. bankin yana nesa da garin amma zaka iya zuwa gurin akan lokaci idan kabi ta hanyar Tudun wada.

 17. Buƙatar
 18. Mastering a new language takes a lot of time and efforts. ƙwarewa a sabon yare yana buƙatar lokaci mai tsawo da kuma bada himma sosai.
 19. Ɗaukan tsawon lokaci
 20. How long does it take to build a new house? tsawon wani lokaci zai ɗauka a kammala gina sabon gida?

  It takes two months to build a house from scratch. wata biyu yake ɗauka a gina sabon gida.

  Journey from Kano to Zaria takes two hours. tafiya daga Kano zuwa Zaria tana ɗaukar sa'o'i biyu.

  It took three hours to fix the phone. ya ɗauki sa'o'i uku a gyara wayar.

 21. Shan magani ko ƙwaya
 22. Anti-malarial pills are taken twice a day. ana shan maganin maleriya ne sau biyu a rana.

  Her mother forces her to take the drugs. mahaifiyarta tana tilasta mata shan magungunan.

 23. Yiwa lamari wata iriyar fahimta
 24. We're not taking his desertion from the army as cowardice. bama ɗaukan guduwar da yayi daga aikin soja a matsayin tsoro.

  I intended it as a joke but he took it as an insult. ni wasa nake masa amma sai ya ɗauki abun a matsayin cin fuska.

  If you smile that's means you never take it seriously. idan kana yin murmushi hakan yana nufin baka ɗauki lamarin da muhimmanci ba.

 25. Matsayin mutum akan abu
 26. Someone who is career-oriented with many children may hardly take any affection in his family. mutumin da yafi bawa sana'arsa muhimmanci fiye da komai zai wahala ya wani damu da iyalansa.

  You can hardly keep calm if you take notice of what everybody says. zai yi wahala ka samu natsuwa idan kana damuwa da abunda kowani mutum yake cewa.

  People are more likely to take pity on children and women. mutane sunfi tausayawa yara da kuma mata.

  Many people take the opinion that outgoing people are more experienced than introverts. mutane da dama suna da ra'ayin cewa masu yawace-yawace sun fi masu shuru-shuru wayewa.

 27. Yin bazata
 28. Restrictions in the amount of money you can withdraw from your account took us by surprise. ƙayyade yawan kuɗin da zaka iya cirewa daga cikin asusun ajiyarka na banki ya zo mana a ba-zata.
 29. Karɓe
 30. They kidnapped and took money from them. sun sace su sannan sun karɓe kuɗaɗe a hannunsu.

  Hoodlums are going to take control of the town in the absence of security forces. 'yan iska sune zasu karɓe ikon tafiyar da garin idan babu jami'an tsaro.

 31. Ra'ayin mutum game da abu
 32. What is your take on cashless money transaction? menene ra'ayinka akan yin siyayya ba tare da amfani da takaddun kuɗi ba?

  Synonyms (kalmomi masu alaƙa)
  opinion, point of view

 33. Aikata wani abu
 34. It's time to take a break. lokacin da zamu je hutu yayi.

  We usually take a rest after every ten hours. mun kasance muna zuwa hutu duk bayan awa goma.

  You can take a walk if can't wait for the bus. zaka iya takawa idan baza ka iya jiran motar ba.Probably Related words: mistake, mistaken, intake, overtake, retake, stake, take away, taken, takeover, betake

Nearest words:
taken, take off, takeaway, takeover, take away, take time, take your time, take the high road, take the offensive, take sth into account,


English Hausa Dictionary/Kamus

English to Hausa Words list

A-B-C-D-E-F-G-H-I-J-K-L-M-N-O-P-Q-R-S-T-U-V-W-X-Y-Z

Hausa to English Words list

A-B-Ɓ-C-D-Ɗ-E-F-G-H-I-J-K-Ƙ-L-M-N-O-R-S-T-U-W-Y-'Y-Z

Kamus.com.ng is an online/offline English to Hausa And Hausa to English comprehensive bilingual Dictionary (or Kamus in Hausa) containing thousands of British and American English words/phrases and Abbreviations.

The website/app provide definition of any existing English or Hausa word and phrase.

Each words came along with parts of speech.

We included hausa descriptions of complex and ambiguous definitions

We specified British Audio and IPA pronunciation of any English word for those wishing to know how to pronounce a particular word.

We provide English & Hausa bilingual usage sentences, description images, audio pronunciations of all Hausa words, pluralization of Hausa words, and origins of Hausa words derived from Arabic or English.

However this website came along with English to Hausa learning resources designed specifically for native Hausa wishing to learn English as second language.

Scientific words, medical words, geology, geography, biology, anatomy, chemistry, physics, literature, computing, psychology and linguistics words were included and precisely translated to Hausa.

Enjoy your stay here and also contribute to its growth by linking to us or inform others about this website.

The dictionary is frequently being updated and it works both online and offline.

If there is any missing word in the dictionary please send us the word and we'll add the word as soon as possible

Aika Zuwa

Whatsapp

Copyright © 2014-2024 kamus.com.ng. All rights reserved