meaning of put in Hausa | Hausa Dictionary | English Hausa Dictionary
kamus
Hausa Dictionary
Our App | Koyon Turanci |Quran Search


Definition of put in Hausa

put

verb /pʊt/
1. Sanya, sawa
2. Rubuta abu
3. Anfani da kalma a cikin magana
4. put a price/value/figure on something: sanyawa abu farashi, kimanta darajan abu
5. Sanya mutum ko abu a cikin wani yanayi
6. Kawo, janyo
7. Yanke hukunci akan yadda abu zai kasance ta hanyar kwatanta shi da sauran abubuwa makamanta

Example of put in a sentence

 1. Sawa, sanya
 2. Put the mobile phone down here. a sanya wayar salular anan ƙasa.

  Did you put sugar in my tea? ko ka sanya sikari a cikin shayi na?

  Put your name here. sanya sunanka anan gurin.

  He put sugar into the gruel. ya sanya sikari a cikin kunun.

  She put her bag on the bed. ta sanya jakarta akan teburi.

  You may hardly see her put her hands over his shoulder in public. zai yi wahala ka ganta ta sanya hannu a kafaɗar shi a cikin jama'a.

  She put her hands around the door. ta sanya hannunta a kewayen ƙofar.

  This bag isn't big enough to put everything together. jakar bata da girman da za'a iya sanya komai a ciki.

 3. Yin rubutu
 4. Put question mark after the paragraph. ka sanya alamar tambaya bayan sakin layin.

  It will be nice if they put English translation. zai fi dacewa idan da sun rubuta fassara ta turanci.

 5. Anfani da kalma a cikin magana
 6. I wish to ask her for help, but i didn't know how to put it in sentence as i'm not fluent in English. naso na nemi taimako daga gareta, amma ban san yadda zan gaya mata ba saboda ban ƙware a turanci ba.

  As wise people put it, "no condition is permanent". kamar yadda masu iya magana suke cewa "babu wani abu a rayuwa da yake dawwama".

  You're free to put your point of view. ƙofa a buɗe take ka faɗi ra'ayinka.

 7. Sanya farashi ko kimanta daraja
 8. He put a price of two million naira on his website. ya sanyawa shafin yanar shi kuɗi har naira miliyan biyu.

  Can you put a value on parenting? shin zaka iya kimanta darajan da zama iyaye yake dashi?

 9. Sanya mutum ko abu cikin wani yanayi
 10. The general put the soldiers at risk by sending them to fight insurgents without heavy weapons. shugaban rundunar ya sanya sojojin cikin haɗari ta hanyar aika su su yaƙi 'yan tawaye ba tare da manyan makamai ba.

  He received death sentence and put to death thereafter. an yanke mashi hukunci kisa sannan daga bisani aka kashe shi.

  Death of his parents put him in a very difficult position. mutuwar iyayen shi sun sanya shi cikin mawuyacin yanayi.

  Occupation of the country failed to put a democratic government. mamaye ƙasar ya gaza kaiwa ga sanya gwamnatin dimukraɗiya.

  There's no way to put broken glasses back to normal without recycling once disintegrated. babu yadda za'a yi ka sake mayar da gilashin daya fashe ya koma dai dai ba tare da an sake sarrafa shi ba.

  I have an idea but i need financial support to put it into practice. ina da abun dana ke son ƙirƙira amma ina buƙatar tallafin kuɗaɗe domin aiwatar dashi.

  He was sentenced and put on trial for corruption. an yanke mashi hukunci kuma an sanya shi a waƙafi saboda cin hanci da rashawa.

  He put his daughter's date of birth in his mind. ya sanya ranar haihuwar 'yar shi a ranshi.

  Financial crisis put people under pressure to revise their budgets. matsalar kuɗaɗe tana sanya mutane cikin matsi ta yadda har sai sun sauya yanayin kashe kuɗaɗen su.

 11. Kawo, janyo
 12. He's cruel in his youth, but he put his faith in God and treat people with respect when his health deteriorated as he approached old age. lokacin da yake saurayi shi mugu ne, amma yanzu ya koma yana mayar da lamurran shi zuwa ga Allah bayan yanayin lafiyar shi ta taɓarɓare lokacin daya fara tsufa.

  Most people put their faith in any religion their parents rise them even if it doesn't make sense. yawancin mutane suna yin imani da duk wani addini da iyayen su suka horar dasu akai koda kuwa wannan addinin bashi da ma'ana.

  Kaduna state government restricted social gathering and puts a lot of emphasis on facemask. gwamnatin jihar Kaduna ta taƙaita yawan taron jama'a sannan tana ƙarfafa yin anfani da takunkumin rufe fuska.

  He's responsible for the collapse of the wall but still he put the blame on the contractor. shine yake da alhakin rushewar ginin amma duk da haka sai ya ɗaura laifin akan ɗan kwangilan.

  Federal government put tax on most imported goods with the exemption of foodstuffs. gwamnatin tarayya ta sanya haraji akan yawancin kayayyakin da ake shigo dasu, amma banda kayan abinci.

  Government put millions of naira into power sector for years, but no significant progress has been made. gwamnati tana sanya miliyoyin kuɗaɗe a ɓangaren samar da lantarki tun shekaru aru aru, amma har yanzu ba'a samu wani cigaba na azo agani ba.

  The current President managed to put an end to insurgency in the country. shugaban ƙasar na yanzu ya samu nasarar kawo ƙarshen tawaye a ƙasar.

 13. Yanke hukunci ta hanyar kwatanci
 14. Alexa put Google as top one most visit website in the world. kanfanin Alexa ya sanya google a matsayin shafin yanar gizo wanda aka fi yin anfani dashi a duniya.

  He puts the needs of his family above career. yana fifita buƙatun iyalan shi akan sana'arshi.

  Please don't rush, try to keep the issues in perspective. kada kayi gaggawa, kayi ƙoƙarin ganin komai sun kasance yadda ya kamata.

  Seeking professionals help can often help to put your own problems into perspective. neman taimakon ƙwararru zai taimaka gurin gano yadda za'a shawo kan matsalolinka.


Probably Related words: computer, deputy, dispute, computerize, computing, input, amputate, disputant, output, reputation

Nearest words:
put it about, put your back into something, put ideas into somebody's head, put something out of your mind, put yourself in sb's place, position or shoes,


English Hausa Dictionary/Kamus

English to Hausa Words list

A-B-C-D-E-F-G-H-I-J-K-L-M-N-O-P-Q-R-S-T-U-V-W-X-Y-Z

Hausa to English Words list

A-B-Ɓ-C-D-Ɗ-E-F-G-H-I-J-K-Ƙ-L-M-N-O-R-S-T-U-W-Y-'Y-Z

Kamus.com.ng is an online/offline English to Hausa And Hausa to English comprehensive bilingual Dictionary (or Kamus in Hausa) containing thousands of British and American English words/phrases and Abbreviations.

The website/app provide definition of any existing English or Hausa word and phrase.

Each words came along with parts of speech.

We included hausa descriptions of complex and ambiguous definitions

We specified British Audio and IPA pronunciation of any English word for those wishing to know how to pronounce a particular word.

We provide English & Hausa bilingual usage sentences, description images, audio pronunciations of all Hausa words, pluralization of Hausa words, and origins of Hausa words derived from Arabic or English.

However this website came along with English to Hausa learning resources designed specifically for native Hausa wishing to learn English as second language.

Scientific words, medical words, geology, geography, biology, anatomy, chemistry, physics, literature, computing, psychology and linguistics words were included and precisely translated to Hausa.

Enjoy your stay here and also contribute to its growth by linking to us or inform others about this website.

The dictionary is frequently being updated and it works both online and offline.

If there is any missing word in the dictionary please send us the word and we'll add the word as soon as possible

Aika Zuwa

Whatsapp

Copyright © 2014-2023 kamus.com.ng. All rights reserved