meaning of on in Hausa | Hausa Dictionary | English Hausa Dictionary
kamus
Hausa Dictionary
Our App | Koyon Turanci |Quran Search






Definition of on in Hausa

on

preposition & adverb /ɒn/ a kai, a jiki, kusa da, gab da, bisa, kunna

Example of on in a sentence

  1. Kai, jiki
  2. Many books are on the table. akwai littafai da yawa akan teburi.

    I placed the computer on top of the bed beyond children's reach. na sanya kwamfutar a saman gado gurin da yara baza su iya cimmata ba.

    There are marks on her skirt. akwai alama a jikin bujanta.

    Please hang this poster on the board. ɗan liƙa wannan fostar a jikin allo.

  3. Hanyar sufuri
  4. People rarely travel on trains in Nigeria. mutane basu cika yin tafiya ta jirgin ƙasa ba a Naijeriya.

    Can you go to Kano from Zaria on a bike? shin zaka iya zuwa Kano daga Zaria akan keke?

    I can even get there on foot. zan iya ma zuwa gurin da ƙafa.

  5. Lokacin aukuwa
  6. She stays at home on Saturday. tana zama a gida ranar Asabar.

    I'm going to Kano on Monday. zan je Kano ranar Litinin.

    The election was scheduled to take place on 1st November. an tsara zaɓen ne domin ya gudana a ranar ɗaya ga watan 11.

    I saw him on the day you arrived. na ganshi a ranar daka zo

    I've visited Kano on several occasions. na ziyarci Kano a lokuta da dama.

    The two suspects have been seen together on two separate occasions. waɗanda ake zargin an gansu tare a lokuta biyu mabanbanta.

    The President of the country traveled abroad on three seperate occasions within one month. Shugaban ƙasar yayi tafiya ƙasar waje karo uku a cikin wata ɗaya.

    On the evening of Monday 2nd of November. da maraicen ranar Litinin biyu ga watan Nawamba.

  7. Abu na kan wakana
  8. Rioters set many banks on fire during the protests. masu tada-zaune-tsaye sun cinnawa bankuna da yawa wuta lokacin zanga zangar.

    We are on duty. muna fagen aiki.

    The registration is on progress. a halin yanzu ana kan yin rijistar.

  9. Gurin naɗa da watsa bayanai
  10. I store all my photos on memory card. ina ajiye dukkan hotunana a katin naɗan bayanai.

    The news was published on the internet. an watsa labarin ne a duniyar gizo.

  11. Samun rauni ko bugewa da abu
  12. Be careful or else you will hit your head on the door. kayi hankali idan ba haka ba zaka bige kanka a jikin ƙofar.

    Don't allow a child to play with sharp object or else he will cut himself on it. kada ka bar yaro yana yin wasa da abu mai kaifi idan ba haka ba to zai yanke kansa.

    I pricked and injured myself on a needle. na yiwa kaina rauni da allura.

  13. Jiɓanci wani lamari
  14. A speech on economy. magana akan tattalin arziki.

    What did she said on the matter? me tace akan lamarin?

  15. Kashe kuɗi akan abu
  16. I spend half of my salary on food. ina kashe rabin albashina gurin siyan abinci.

    Wasting money on expensive clothes. ɓannatar da kuɗaɗe gurin siyan suturu masu tsada.

    Banks pay 10% interest per annun on the savings account. banki suna bada ribar kashi goma cikin ɗari na yawan kuɗin daka ajiye a asusun banki a shekara.

  17. Dogara ga
  18. You can't financially rely on your parents for ever. baza ka iya dogara ga iyayenka gurin samun kuɗi ba har abada.

    Future of our country depends on this election. makowar ƙasarmu ta dogara ne akan wannan zaɓen.

    We write a book based on the culture of our audience. muna rubuta littafi ne bisa ga al'adun masu karanta littafin namu.

    Dogs and cats can live on grains or meat. karnuka da maguna zasu iya dogara ga hatsi ko nama a matsayin abinci.

    Likewise some machines run on kerosene or diseal. hakama wasu injinan zasu iya yin aiki da kalanzir ko man diseal.

    The sex worker is always on drugs. a koda yaushe karuwar tana shan magani (na hana ɗaukar ciki).

  19. Jikin, kusa da, gab da
  20. Registration office is on bank entrance. ofishin yin rijistar yana daidai ƙofar banki.

    Most banks in Zaria are located on PZ Street. yawancin bankuna dake Zaria suna layin PZ ne.

    There is a lake on the border between Nigeria and Chad. akwai tafki a mararrabar dake tsakanin Naijeriya da ƙasar Chadi.

  21. Lokacin da mutum yake cikin wata tsangaya
  22. Bello and Yahya are on the country's football team. Bello da Yahya suna cikin ƙungiyar dake wakiltar ƙasar.

    There are only twenty people on the team. mutane goma ne kawai a ƙungiyar.

  23. Aiki da abu
  24. You can browse the Internet on mobile phones. zaka iya shiga duniyar gizo ta hanyar yin amfani da wayar tafi da gidanka.

    I talked to him on the phone. tayi masa magana ta waya.

  25. Faruwa daga bisani
  26. He was kidnapped along Kaduna to Abuja highway on his return from work. an sace shi a hanyar Kaduna zuwa Abuja a lokacin da yake hanyar dawowa daga aiki.
  27. Kunna
  28. Please switch on the fan. ɗan kunna fankar.

    I already turned it on. na riga na kunna.

    Make sure you always leave it on even in the morning. to ka tabbatar da cewa ka bar ta a kunne koda kuwa da safiya ne.


Probably Related words: Calculation, caption, carbon, carton, caution, celebration, chronic, coconut, colony, combination

Nearest words:
one, once, Ondo, only, onto, onion, onset, on top, oneway, online,


English Hausa Dictionary/Kamus

English to Hausa Words list

A-B-C-D-E-F-G-H-I-J-K-L-M-N-O-P-Q-R-S-T-U-V-W-X-Y-Z

Hausa to English Words list

A-B-Ɓ-C-D-Ɗ-E-F-G-H-I-J-K-Ƙ-L-M-N-O-R-S-T-U-W-Y-'Y-Z

Kamus.com.ng is an online/offline English to Hausa And Hausa to English comprehensive bilingual Dictionary (or Kamus in Hausa) containing thousands of British and American English words/phrases and Abbreviations.

The website/app provide definition of any existing English or Hausa word and phrase.

Each words came along with parts of speech.

We included hausa descriptions of complex and ambiguous definitions

We specified British Audio and IPA pronunciation of any English word for those wishing to know how to pronounce a particular word.

We provide English & Hausa bilingual usage sentences, description images, audio pronunciations of all Hausa words, pluralization of Hausa words, and origins of Hausa words derived from Arabic or English.

However this website came along with English to Hausa learning resources designed specifically for native Hausa wishing to learn English as second language.

Scientific words, medical words, geology, geography, biology, anatomy, chemistry, physics, literature, computing, psychology and linguistics words were included and precisely translated to Hausa.

Enjoy your stay here and also contribute to its growth by linking to us or inform others about this website.

The dictionary is frequently being updated and it works both online and offline.

If there is any missing word in the dictionary please send us the word and we'll add the word as soon as possible

Aika Zuwa

Whatsapp

Copyright © 2014-2024 kamus.com.ng. All rights reserved