meaning of have in Hausa | Hausa Dictionary | English Hausa Dictionary
kamus
Hausa Dictionary
Our App | Koyon Turanci |Quran Search
English To Hausa Hausa To English© Copyright 2014-2023 Shamsuddeen Inc. All right reserved

Definition of have in Hausa

have

auxiliary verb /hæv/,/həv/,/əv/
1. Ana yin anfani dashi tare da past participle domin samar da present perfect da kuma past perfect

verb /həv/
2. Kasancewa kana da abu
3. Kamuwa da rashin lafiya
4. Aikata abun da aka ambato
5. Cin abinci ko shan abin sha
6. Samu ko yarjewa
7. Fama da matsalar da wani ya janyo maka
8. Fuskantar wani abu
9. Haihuwan jariri

modal verb /həv/
10. have to do sth: idan akwai buƙatar ayi wani abu

Example of have in a sentence
 1. Ana yin anfani dashi domin samar da present perfect da past perfect
 2. I've received my January salary. albashi na na watan Janairu ya iso gareni.

  Zulaihat hasn't returned yet. Zulaihat bata dawo ba tukunna.

  I haven't ever used IPhone in my lifetime. ban taɓa yin anfani da wayar IPhone ba a rayuwa ta.

  Have you exhausted your Salary? shin ka gama kashe albashin ka?

  Has she graduated from university? shin ta kammala karatun jami'a?

  Despite the interrogation, the police hadn't had any information from the suspect. duk da tatsan bayanan da aka yi, 'yan sandan basu samu wani bayani daga gurin wanda ake zargin ba.

 3. Kasancewa kana da abu
 4. Nigeria have abundant natural resources. Nigeria tana da tarin ma'adanan ƙarƙashin ƙasa.

  Although he's busy, i think he has time for browsing the internet. duk da cewa akwai ayyuka a gaban shi, ina tinanin yana da lokacin shiga duniyar gizo.

  You can come to witness what happened if you have time. zaka iya zuwa ka shaida abun daya faru idan ka samu lokaci.

  She has got experience working for the company. ta samu gogewa da take yin aiki a kanfanin.

 5. Kamuwa da rashin lafiya
 6. Three doctors had covid-19. likitoci uku sun kamu da cutar nunfashi.

  I've got malaria fever. na kamu da cutar malaria.

 7. Aikata abun da aka ambato
 8. Ask him to have a bath. ka buƙace shi da yayi wanka.

  I had a bath this morning. nayi wanka da wannan safiyar.

  We had a conversation with her yesterday. mun yi fira da ita jiya.

  I usually have a rest when i tired? a duk lokacin dana gaji ina hutawa.

 9. Cin abinci ko shan abun sha
 10. I had rice and beans for breakfast. zanyi karin kumallo da shinkafa da wake.

  I'm thirsty, please let me have some water. ina jin ƙishi ɗan bani ruwa.

 11. Samu ko yarjewa
 12. Have a wife, she'll calm your nerves. ka samu mata, zata kwantar maka da hankali.

  Let me have one more orange. ina buƙatar a bani ƙarin lemu ɗaya.

 13. Fama da matsalar da wani ya janyo maka
 14. She had her head cut off. an fille mata kai.
 15. Fuskantar wani abu
 16. We receive our monthly salary each month, we didn't have any problem thereof. muna samun albashin mu duk wata, bamu samun wata matsala game da wannan.

  She is the only person who hasn't been having much luck. ita ce kawai wacce bata samun sa'a.

 17. Haihuwan jariri
 18. Zulaihat had her baby in January. Zulaihat ta haifi jaririnta a watan Janairu.

  My parents had me in their twenties. iyayena sun haife ni ne lokacin da suke shekara ishirin da wani abu.

 19. Buƙatar kayi wani abu
 20. I have to focus on my study to pass the examination. akwai buƙatar na mayar da hankali akan karatu na domin cin jarabawa.

  What do you have to achieved before you turned 30? me ya kamata ace ka samu kafin ka cika shekaru talatin?

  Do you have to stay with us tonight? shin akwai buƙatar ka tsaya tare damu da dare?

  We'll have to start saving for sallah festival. akwai buƙatar mu fara tara kuɗaɗe domin yin bikin sallah.

  I suffer from headache so I've to stay at home today. ina fama da ciwon kai don haka ya kamata na tsaya yau a gida.

English Hausa Dictionary/Kamus

English to Hausa Words list

A-B-C-D-E-F-G-H-I-J-K-L-M-N-O-P-Q-R-S-T-U-V-W-X-Y-Z

Hausa to English Words list

A-B-C-D-E-F-G-H-I-J-K-L-M-N-O-R-S-T-U-W-Y-Z

Kamus.com.ng is an online/offline English to Hausa And Hausa to English comprehensive bilingual Dictionary (or Kamus in Hausa) containing thousands of British and American English words/phrases and Abbreviations.

The website/app provide definition of any existing English or Hausa word and phrase.

Each words came along with parts of speech.

We included hausa descriptions of complex and ambiguous definitions

We specified British Audio and IPA pronunciation of any English word for those wishing to know how to pronounce a particular word.

We provide English & Hausa bilingual usage sentences, description images, audio pronunciations of all Hausa words, pluralization of Hausa words, and origins of Hausa words derived from Arabic or English.

However this website came along with English to Hausa learning resources designed specifically for native Hausa wishing to learn English as second language.

Scientific words, medical words, geology, geography, biology, anatomy, chemistry, physics, literature, computing, psychology and linguistics words were included and precisely translated to Hausa.

Enjoy your stay here and also contribute to its growth by linking to us or inform others about this website.

The dictionary is frequently being updated and it works both online and offline.

If there is any missing word in the dictionary please send us the word and we'll add the word as soon as possible

Aika Zuwa

Whatsapp

© Copyright 2014-2023 Shamsuddeen Inc. all right reserved