meaning of day in Hausa | Hausa Dictionary | English Hausa Dictionary
kamus
Hausa Dictionary
Our App | Koyon Turanci |Quran Search


Definition of day in Hausa

day

noun /deɪ/
1. Rana
2. Yini
3. Day off: ranar hutu
4. The other day: kwanaki kaɗan da suka wuce
5. These days: a 'yan kwanakin nan
6. In those days: a lokutan baya
7. Any day now: bada jimawa ba
8. Day after day: akai-akai, koda yaushe
9. Day and night: koda yaushe
10. Day by day: kowace rana, sannu a hankali
11. The days: zamani, wani lokaci a tarihi
12. To this day: har ila yau, har yanzu

Example of day in a sentence

 1. Rana
 2. You have three days left. kwanaki uku suka rage maka.

  Days of the week. kwanakin cikin mako.

  He goes to the gym every day. yana zuwa gidan motsa jiki kowace rana.

  We can hardly watch all the movies in a day. zai yi wahala mu gama kallon dukkan fina-finan a cikin rana guda.

  I got married the day before yesterday. nayi aure shekaranjiya.

  We are going to Kano to buy a car the day after tomorrow. zamu je Kano mu sayo mota jibi.

  He relocated to Zaria five days ago. kwananshi biyar kenan da dawowa Zaria.

  He is looking for his son who left home and haven't been seen for three days. yana neman ɗansa wanda ya bar gida kuma kwana uku kenan ba'a ganshi ba.

  Working day. ranar aiki.

 3. Yini
 4. I don't like to go out in a sunny day because I can't endure the heat. bana son fita a lokacin da akwai zafin zana saboda bazan iya jurewa zafin ba.

  Business owners complain they don't have a lot of sales if it rained all day without interruption. 'yan kasuwa suna yin ƙorafin cewa basa samun ciniki sosai idan aka shafe tsawon yini ana yin ruwan sama ba ƙaƙƙautawa.

  I sleep during the day because I study a lot in the night. ina yin bacci da rana saboda ina yin nazari sosai da dare.

 5. Ranar hutu
 6. Please visit her if you have a day off. don Allah ka ziyarce ta idan ka samu ranar hutu.

  Don't worry I will take two days off to visit her. kada ka damu zan nemi hutun kwana biyu domin na ziyarce ta.

 7. Kwanaki kaɗan da suka wuce
 8. Are you the one I saw the other day? shin kaine wanda na gani kwanan baya?

  I parked my car in front of the bank the other day. na yi fakin ɗin motata a gaban bankin kwanakin baya.

  I stayed at home sleeping the other day. kwanakin baya na tsaya ne a gida ina yin bacci.

  He waited here in the other day and talked to us. ya tsaya a nan kwanakin baya yayi mana magana.

 9. A 'yan kwanakin nan, a halin yanzu
 10. Typhoid fever is extremely rare in Nigeria these days. a 'yan kwanakin nan ba'a cika samun masu kamuwa da zazzaɓin typhoid ba a Nigeria.

  These days people are aware of the dangers behind drinking unclean water. a 'yan kwanakin nan mutane suna ankare da hatsarin dake tattare da shan ruwa mara tsafta.

  Any bank has ATM machine in Nigeria these days. a halin yanzu kowani banki a Nigeria yana da na'urar zarar kuɗi.

  You can't stay unemployed and expect your parents to pay your bills these days. a wannan zamanin ba zai yuwu ka ƙi yin aiki ba kana jiran iyayenka suna ɗaukan nauyinka.

  These days, younger generation find it difficult to differentiate between Hausa and Fulani. a wannan zamanin matasa basu cika iya bambamce bahaushe da bafulatani ba.

 11. A lokutan baya
 12. In those days few people can read and write in the country. a shekarun baya mutane ƙalilan ne zasu iya yin rubutu da karatu a ƙasar.

  In those days girls are being married off at very young age. a wancan lokacin ana yiwa yara mata auren wuri.

  People did not appreciated the impact of education in those days. mutane basu san alfanun ilimi ba a wancan zamanin.

 13. Bada jimawa ba
 14. The new factory would be launched any day now. bada jimawa ba za'a buɗe sabuwar ma'aikatar.

  "When are you going to travel abroad?" "Any day now!" "Yaushe zaka yi tafiya ƙasar waje?" "Bada jimawa ba!"

  He is coming back any day now. zai dawo bada jimawa ba.

  He is going to buy you a gift any day now. bada jimawa ba zai siya kyauta ya baka.

 15. Akai-akai, koda yaushe
 16. We experience similar problems day after day. matsala iri ɗaya muke fuskanta koda yaushe.

  Day after day, he gains confidence in making public speaking. a kowace rana yana ƙara samun zarran yin magana a bainar jama'a.

  The symptoms of the desease would be reduced day after day till you recovered completely. sannu a hankali alamomin ciwon zai ta raguwa har sai ka warke gabaki ɗaya.

  It's the same type of film they show day after day. shirin film iri guda ne suke haskawa koda yaushe.

  He gives her the same advice day after day. shawara iri guda yake bata koda yaushe.

  The noise is persistence day and night. a koda yaushe ana jin ƙaran.

 17. Kowace rana, sannu a hankali
 18. Day by day we accumulated more resources. mun tara dukiya sannu a hankali.

  English words are being assimilated into Hausa day by day. sannu a hankali kalmomin ingilishi suna shigewa cikin harshen Hausa.

  The tree grows day by day. kullum bishiyar tana ƙara girma.

  Hatred towards the government is increasing day by day. ƙiyayyar da ake nunawa gwamnati na ƙaruwa a koda yaushe.

  Our sales declined and keep reducing day by day. cinikinmu yayi ƙasa kuma yana cigaba da raguwa kulla yaumun.

  Day by day, my love for education grow higher. a koda yaushe son da nake yiwa ilimi daɗuwa yake yi.

 19. Zamani
 20. The day of your criminal activities is over. zamanin yin ta'addancinku ya wuce.

  The days before computer people rely on libraries to conduct their research. lokacin da babu kwanfuta mutane sun dogara ne ga ɗakin karatu domin yin bincikensu.

  How do people cope with mosquito in the days before anti-malarial drugs was invented? yaya mutane suke fama da sauro lokacin da babu maganin Malaria?

  The days of war among Hausa kingdoms is over. lokacin yaƙi tsakanin masarautun Hausawa ya wuce.

  Our currency value has not appreciated since the days of military regimes. darajan kuɗinmu bai ƙaru ba tun lokacin mulkin soji.

 21. Har ila yau, har yanzu
 22. To this day he don't have enough confidence to make public speaking. har yanzu bashi da ƙwarin gwiwan da zai iya yin jawabi a cikin jama'a.

  He is that kind of person who to this day, don't appreciate little things in life. shine irin wannan mutumin wanda har yau bashi da godiya.

  She was molested at young age, but to this day, she feels hatred toward her abuser. tun lokacin tana ƙarama aka keta mata haddi amma har yanzu tana jin haushin wanda yayi mata wannan abun.

  To this day, many people think she's single. har yanzu mutane suna tunanin cewa bata da aure.


Probably Related words: Friday, holiday, Saturday, Sunday, yesterday, today, Tuesday, Wednesday, birthday, everyday

Nearest words:
day off, day care, daybreak, daydream, day by day, day after day, day and night, day care center, days are numbered,


English Hausa Dictionary/Kamus

English to Hausa Words list

A-B-C-D-E-F-G-H-I-J-K-L-M-N-O-P-Q-R-S-T-U-V-W-X-Y-Z

Hausa to English Words list

A-B-Ɓ-C-D-Ɗ-E-F-G-H-I-J-K-Ƙ-L-M-N-O-R-S-T-U-W-Y-'Y-Z

Kamus.com.ng is an online/offline English to Hausa And Hausa to English comprehensive bilingual Dictionary (or Kamus in Hausa) containing thousands of British and American English words/phrases and Abbreviations.

The website/app provide definition of any existing English or Hausa word and phrase.

Each words came along with parts of speech.

We included hausa descriptions of complex and ambiguous definitions

We specified British Audio and IPA pronunciation of any English word for those wishing to know how to pronounce a particular word.

We provide English & Hausa bilingual usage sentences, description images, audio pronunciations of all Hausa words, pluralization of Hausa words, and origins of Hausa words derived from Arabic or English.

However this website came along with English to Hausa learning resources designed specifically for native Hausa wishing to learn English as second language.

Scientific words, medical words, geology, geography, biology, anatomy, chemistry, physics, literature, computing, psychology and linguistics words were included and precisely translated to Hausa.

Enjoy your stay here and also contribute to its growth by linking to us or inform others about this website.

The dictionary is frequently being updated and it works both online and offline.

If there is any missing word in the dictionary please send us the word and we'll add the word as soon as possible

Aika Zuwa

Whatsapp

Copyright © 2014-2024 kamus.com.ng. All rights reserved