Shin turanci yare ne mai sauƙin koyo? Amsar itace,
Wani misalin kuma shine akwai yaruka sama da ɗari da hamsin a yankunan arewacin Nigeria, yammacin jamhuriyar niger da kuma tsakiyan ƙasashen Kamaru da Cadi; Waɗanda suke cikin rukunin harshe ɗaya da Hausa wato Chadic languages, idan kun duba zaku ga cewa yawancin masu amfani da waɗannan harsunan suna matuƙan samun sauƙin koyon harshen hausa saboda fasali da kuma salon waɗannan harsunan duk iri ɗaya ne da hausa, hasalima idan kuka yi waiwaye zaku ga cewa masana ilimin lafazi wato linguistics sun yi ittifaƙin cewa waɗannan yarukan duk yare ɗaya ne waɗanda suka samo asali daga rukunin harsunan Afro-asiatic, daɗewan lokaci ne yasa suka rarrabu. Don haka mutanen da harsunan su na gado sune Ngas, Marghi, Karekare da sauransu zasu ga cewa suna samun sauƙi gurin ƙwarewa a harshen Hausa. Sannan kuma masu amfani da waɗannan harsunan na Chadic languages zasu samu sauƙin koyon harsunan Semitic languages (misali harsunan larabci, Hebrew, Aramaic da Amharic) saboda Chadic languages kaman dai shi Larabci da Hebrew suna cikin rukunin harsunan Afro-asiatic languages ne. Na tabbata idan cikin masu karanta wannan maƙalar akwai waɗanda suka iya larabci zasu fahimci cewa larabci yana da matuƙar sauƙin koyo ga mutanen da Hausa, Marghi, Ngamo, Bade ko Karekare sune harshen su na gado, domin waɗannan harsunan duk sun samo asaline guri ɗaya da harshen Larabci. Misalin kuwa shine idan kun duba zaku ga cewa Harsunan Hausa da larabci suna da kamanceceniya dangane da haruffan da suke amfani dasu gurin banbance mace da namiji. misali, hausawa da larabawa duk suna amfani da 'ka' domin nufin namiji. sannan duk suna amfani da 'ki' domin nufin mace. misali da Hausa muna cewa 'me sunan ka?' da larabci kuma muce 'maá ismu ka?'. Har ila yau kuma da Hausa muna cewa 'me sunan ki?', sannan kuma da larabci muce 'maá ismu ki?'. Hakazalika Hausawa da larabawa duk suna amfani da 'ya' domin nufin namiji, da kuma 'ta' domin nufin mace. Misali Hausawa na cewa 'ta na gudu', larabawa kuma suce 'tarkudu'. Sannan kuma Hausawa na cewa Yana gudu. Sannan Larabawa suce Yarkudu.
A yanayin yanda tinanin mutane yake, mutane sun kasance suna kwaikwayon salon harshen su na gado ne a yunƙurin koyon amfani da kalmomi domin haɗa jimla a wata sabuwar yare da suke shirin koyo. Hakan ne yasa koyon wani sabon yare yake da matuƙan wahala saboda galibi da akwai banbance banbance masu yawa akan yanda ake haɗa jimla tsakanin wannan yaren da wancan. Misali idan bahaushe sabon koyon turanci ne, zai kasance yana kwaikwayon salon harshen Hausa ne, tunda a Hausa muna cewa 'kashe kuɗi' ko 'kashe lokaci' to akwai yuwuwar idan yazo yin magana da turanci ma zai iya cewa 'kill money' ko 'kill time' a maimakon 'spend money' da 'spend time'. Haka ma bazai iya banbancewa ba gurin furta haruffan 'p' da 'f' saboda a Hausa muna amfani da sautin 'f' ne kawai.
Kasancewar Turancin English shine lingua franca na duk duniya (wato yaren da mutanen da basa jin yaren juna suke amfani dashi domin sadarwa tsakanin su); hakan yasa akwai miliyoyin mutane daga sassa dabam daban na duniya da suke koyon wannan yaren a kowacce rana. Kuma ba kasafai masu koyon turanci sukan kai matakin ƙwarewa na C2 ba. (a duba shafin Matakan koyan turanci domin ƙarin bayani), yawanci basa wuce matakin ƙwarewa na B2, wato simple English kenan, wannan ne yasa turanci mai sauƙi (simple English) shi ne turanci mafi karɓuwa a duniya a halin yanzu. Domin shine turancin da koda mutum bai ƙware a turanci sosai ba zai fahimta
Hanya mafi sauƙi ta koyon turanci koma ta koyan kowani yare itace ta hanyar yin mu'amala da mutanen da suke yin magana da wannan yaren. Idan kuma kana ganin hakan zai yi maka wahala to yanzu akwai fina finan turanci da zaka iya kalla a maimakon yin mu'amala da masu yin magana da turanci. Ka tuna da yanda ka koyi harshen hausa, ta yaya ka koye shi? ka koyi harshen Hausa ne sakamakon zama cikin hausawa. Amma ban bada shawarar yin amfani da finafinan turawa ba domin koyon turanci, domin turawa sun kasance suna yin magana ne da sauri kuma fahimtar maganarsu mai yiwuwa zai ba mai koyon turanci wahala; zai fi dacewa kayi amfani da finafinan Nigeria waɗanda aka yi su da ingantaccen turanci ba waɗanda aka yi su da pidgin English ba. Kuma danace finafinan turanci ina nufin shirin film wanda yake ɗauke da saƙonni (wato drama, actions movies, documentary films da dai sauransu) bawai wanda yake ɗauke da jawabi kawai ba (wato video lectures, tutorial video, quranic tafseer da makamantan haka ). Kallon fina finan turanci zai baka damar alaƙanta ko danganta wani aiki da aka aiwatar da kalmar da aka faɗa lokacin aikata wannan aikin. Mai yiwuwa ka taɓa jin labarin wani bakano wanda ya ƙware a harshen Hindi (yaren ƙasar India) har yake koyar da shi a gidan rediyon Kano, ya rubuta littafai na koyon harshen Hindi da Hausa wanda ni kaina na samu kwafi na wannan littafin. Kuma da ake tambayar shi ta yaya ya koyi wannan yaren, ya nuna cewa ya koyi yaren ne ta hanyar kallon finafinan India
Duk da cewa hanya mafi sauri ta koyon wani yare shine ta hanyar zama cikin masu magana da wannan yaren; To amma duk da haka masana sun dage cewa lalle za'a iya koyan yare ta hanyar bin manhajojin karatu. Hanyoyin kuwa sune kamar haka:
Hanya ta farko
Koyon rubutawa tare da karanta rubutun turanci shine abu na farko da mutum zai fara dashi. A bayan da mutum ya ƙware gurin karantawa tare da rubuta turanci, (misali bayan da mutum ya kammala makarantar firamare) zai iya ɗaukan mutum shekaru biyar wasu ma har zuwa shekaru bakwai kafin mutum ya zama ƙwararre gurin rubutawa tare da yin magana da harshen turanci.
Koda yake ya danganta ga irin horan da mutum ya samu, himmatuwan da yake yi da kuma saurin fahimtar da yake da ita. Don kuwa wasu yaran ma tun suna aji huɗu na makarantun firamare suke ƙwarewa gurin rubutawa tare da karanta rubutun turanci. Don ni kaina na ƙware gurin rubutawa tare da karanta rubutun Hausa lokacin ina aji uku a firamare, sannan kuma na ƙware gurin rubutawa da karanta turanci lokacin ina aji huɗu a firamare. Domin sanin hanyar dana bi domin koyon karatun hausa da turanci ka duba gurin shin zai yiwu mutum ya koyi karatu ba tare da malami ba?
Ina ganin muddin mutum ya himmatu zai iya ƙwarewa a turanci na matakin A1 a cikin shekara ɗaya kawaiKoyon karatu tare da rubuta turanci abu ne mai matuƙan sauƙi ga hausawa waɗanda suka fara koyon karatun Hausa. Don kuwa ina ganin a cikin watanni shida kawai mutum zai iya ƙwarewa gurin rubutawa tare da karanta turancin English. Kuma zaka iya koyon rubutu tare da karanta rubutun turanci da kanka ba tare da malami ba. Domin koyan rubutun turanci ka rika samun wani littafi da aka rubuta shi da turanci sannan ka rika rubuta wannan rubutun a littafin rubutu. Sannan zaka iya koyon karanta rubutun turanci ta hanyar yin amfani da fasahar TTS (wato fasahar da take mayar da rubutu ya koma murya). Zaka iya samun wannan fasahar a shafukan yanar gizo ko a manhajojin wayar tafi da gidanka.
Hanya ta biyu
a bayan da mutum ya ƙware gurin karantawa tare da rubuta Turanci, abu na gaba kuma shine vocabulary, wato sanin ma'anan kalmomin Turanci. A ɗabi'ance, mutane sun kasance suna haddace kalma ce ta hanyar fassarata kai tsaye da yaren da suka fara koyo, wato harshen su na gado. Hakan yasa bahaushe zai yi sauƙin haddace kalmomin Turanci saboda da yawa daga cikin kalmomin Turanci za'a iya fassara su kai tsaye zuwa Hausa.
Hanya ta uku
A bayan da mutum ya haddace kalmomi kuma, abubuwa biyu na gaba kuma waɗanda dole su tafi lokaci guda, sune grammar da kuma comprehension.grammar yana nufin 'nahawu' (wato ƙa'idojin da ake bi gurin yin magana da turanci). Sannan kuma comprehension yana nufin 'fahimtar yanda ake amfani da kalma a cikin jimla'.
Koyon grammar abu ne mai matuƙan sauƙi, idan mutum ya mayar da hankali a cikin wata ɗaya zai iya ƙwarewa a grammar. Abun da nake ganin kawai zai ba mutane wahala shine 'Tenses', ƙwarewa a Tenses mai yiwuwa zai ba Hausawa wahala, saboda a Hausa bamu da yawancin waɗannan Tenses
Hanya ta huɗu
Abu na gaba kuma shine comprehension, wato sanin yanda ake amfani da kalmomi a cikin jimla. comprehension abu ne mai matuƙan wahala, kuma zai iya ɗaukan mutun shekaru uku zuwa biyar kafin yasan yanda ake amfani da kowace kalmar Turanci a cikin jimla. Kalmomin turanci suna ɗaukan ma'anoni mabanbanta kuma ana amfani dasu a sigogi dabam dabam. Misali kalmar provide tana nufin 'samar da' past tense na wannan kalmar shine provided, wato yana nufin abun da aka riga aka samar. To amma kuma duk da haka kuma kalmar provided a wasu lokutan kuma tana nufin 'Matuƙan dai'. Duba misalan wannan kalmar a cikin jimla.
Misali na biyu
Kalmar behind duk da cewa tana nufin 'a baya' ne, to amma fassara wannan kalmar zuwa Hausa abu ne da ba zai yiwu ba, domin takan canza ma'ana a wasu lokutan, ya danganta ga irin jimlar da aka sanya ta a ciki.
Misali:Waɗannan kalmomin biyu somin taɓi ne kawai daga cikin kalmomi masu rikitarwa da za kuyi ta cin karo dasu a cikin turanci, kuma dole mutum yasan yanda ake amfani da kowace kalma kafin ya ɗauki kansa a matsayin ƙwararren masanin Turanci. Wannan ne yasa mutane da yawa zasu daɗe suna koyan turanci, amma duk da haka idan suka ɗauko wani littafin turanci suna karantawa, gabaki ɗaya sai su raina turancin su. Domin na lura mafi yawancin mutane, musamman a Nigeria suna da ɗabi'an son yin magana da turanci mai wahala, domin kawai su birge mutane a riƙa yi masu kallon masu ilimi, to amma kuma idan kaje ka dawo kuma zaka ga suna mayar da kansu tamkar wasu sakarkaru ne. Domin kuwa zasu yi magana amma cikin mutane ɗari da suke sauraren su bai wuce a samu mutane goma da suke fahimtar abun da suke cewa ba, ashe kuwa burgewa bata yi rana ba.
Mafi yawanci nan Nigeria bama ɓata lokacin mu gurin koyon turanci mai tsauri, tun da dai turanci ana koyan shi ne domin sadarwa tsakanin mutane, don haka da zaran mutum ya ɗan iya turancin daya isa ya iya yin mu'amala tsakanin mutane kawai shi kenan.
Yanda ake amfani da kalmomi domin fitar da jimla a turanci galibi ya saba da yanda ake amfani dasu a harsunan Naijeriya.
Wace hanya ce tafi dacewa mutum ya bi domin koyon comprehension?
Hanyar da tafi dacewa abi domin koyan comprehension ita ce karanta littattafan da aka rubutasu da ingantaccen turanci, wannan ya haɗa da littattafan adabi (Novel), jaridu ko mujallu ko kuma shafukan yanar gizo. Amma dai nafi bada shawaran ayi amfani da Novel (littattafan ƙagaggun labarai), kuma dole ne ya kasance da akwai dictionary a kusa da kai saboda yawanci ire iren waɗannan littattafan suna yin amfani da kalmomi masu tsauri. Kuma sannan daga lokaci zuwa lokaci yana da muhimmanci mutum ya riƙa gwada ƙwarewarsa ta hanyar rubuta wani labari da turanci, domin ganin irin ci gaban daka samu a harshen Turancin. Ko kuma hanya mafi sauƙi ma tun da da akwai social network, yin musayar saƙonni da mutanen da suke amfani da ingantaccen turanci zai matuƙan taimakawa mutum ya sabawa ƙwaƙwalwarsa ta fahimci yanda ake amfani da kalma. ko kuma zaka iya yin amfani da webcam (yin fira ido na ganin ido ta internet) da mutanen da suke magana da turanci. Kana zaka iya buɗe shafin Internet kyauta na Blog domin yin rubuce rubuce tare da yaɗa su ga duniya. Sannu a hankali kuma zaka samu ƙwarewa a gurin rubutun insha'i
Abu na biyar
Abu na biyar kuma shine Oral English. Oral English yana nufin 'Turancin baki' wato yanda ake furicin kalmomi. Oral English yana daga cikin abu mafi wahala da mutanen Naijeria suke fama dashi. Ba wai na katse maka hanzari bane, amma dai matuƙan dai a Naijeriya ka girma, to kuwa zai yi wahala ka iya yin magana da turanci ba tare da ansan cewa kai ba bature bane. Misali kuwa da zan baka shine idan wani ƙabila yazo nan arewa daga kudu, kuma yazo ne baya jin Hausa, sai daga baya yazo ya koyi Hausan sakamakon cuɗanya da Hausawa, zaka ga duk da cewa ya ƙware a Hausar, amma da zaran yayi magana sai kasan cewa ba bahaushe bane. To amma kuma sai kaga yaran shi daya haifa a ƙasar Hausa kuma ya girma a cikin Hausawa, shi kuma da zaran yayi magana in ban da kamanni zaka ɗauka bahaushe ne.
To amma duk da haka mutumin Naijeriya zai iya yin magana da turanci a cikin turawa kuma su fahimci abin da yake cewa. Duk da cewa bamu sanya darasin Oral English a cikin wannan shafin namu ba tukunna, to amma zaka iya dubawa a wasu guraren.
Abu mafi muhimmanci a darasin Oral English shine sanin yanda ake furta kalmomi. Wannan ko abu ne mai sauƙi, domin kuwa da zaran kana kokwanto akan yanda ake furta kalma, to abun da zaka yi kawai shine ka duba dictionary. Mafi yawancin dictionary suna rubuta yanda ake furta kowace kalma. ko kuma abu mafi sauƙi yanzu da akwai manhajojin wayoyin salula da suke ɗauke da sautin yanda ake furta kalmomin turanci da zaka iya saurara. Amma yana da muhimmanci ka tabbatar da cewa British pronouncition ne ba American pronouncition ba. Don kuwa da akwai banbance banbance masu yawa tsakanin yanda ake furta kalmomi a Turancin Birtaniya da kuma Turancin Amurka. Turancin Birtaniya shine turancin da muke amfani dashi a Naijeriya ba turancin Amurka ba.
Mafi yawancin kalmomin Turanci yanda ake rubuta su ya banbanta da yanda ake furta su. Misali kalmar knowledge, duk da cewa an sanya haruffan 'k' da 'd' a cikin kalmar, to amma ba'a ambaton waɗannan kalmomin gurin furta wannan kalmar, ana furta wannan kalmar ce da nolej
Haka ma kalmar psychology duk da cewa an sanya harafin 'p' a farkon kalmar, amma duk da haka ba'a ambaton wannan harafin gurin furta kalmar. Kuma duk da cewa a bisa ƙa'ida cho ana furta shi ne a matsayin 'co', amma duk da haka a wannan kalmar ana furta shi ne a matsayin 'ko', don haka ana furta wannan kalmar ce da saikoloji.
Wannan kaɗan kenan daga cikin kalmomi masu rikitarwa da dole sai mutum ya iya furta kowace kalma ta turanci kafin ya ɗauki kansa a matsayin ƙwararren masanin Turanci.
ƙwarewa a turanci abune mai yiwuwa, to amma sai an jure, don kuwa indai har mutum ba ɗan baiwa bane, bazai yiwu ya iya ƙwarewa a turanci dare ɗaya ba. Sai dai shi turanci ya kasance ana samun ƙwarewa a kan shine sannu a hankali. Don kuwa ko ni kaina ban koyi turanci a cikin gajeran lokaci ba, don ko yanzu idan nayi waiwaye zuwa ga tsofaffin rubuce rubucen dana ke tayi da turanci a shafukan Facebook, sannan naga irin turancin da nayi amfani dasu a wancen lokutan, sai nayi murmushi idan naga irin kurakuren danai ta tafkawa a wancen lokutan.
Aika Zuwa
© Copyright. Shamsuddeen Zakariya. All right reserved.