Masana harshe sun karkasa zurfin ƙwarewa a harshe zuwa matakai shida ne kamar haka
A1 (Beginners level)
Wannan shine matakin farko, mutumin da yake da ƙwarewa a harshe na matakin A1 zai iya fahimta tare da yin anfani da kalmomi ko jimloli da ake yin anfani dasu yau da kullum. Zai iya zuwa wani guri tare da yin tambayoyi ko amsa tambayoyi masu sauƙi.
A2 (Elementary English)
Mutumin da yake da ƙwarewa ta A2 a harshe zai iya yin anfani tare da fahimtar kalmomin da ake yawan yin anfani dasu a ɓangaren da suka shafi iyalai, yin siyayya, maganganun da ake yin anfani dasu a cikin gari ko gurin aiki. Zai iya yin mu'amala ta yau da kullum da mutane, zai iya yin bayani mai sauƙi akan asalin shi.
B1 (Intermediate English)
Mutumin da yake da ƙwarewa ta B1 a harshe zai iya fahimtar maƙasudin abun da ake yin magana a kai kuma zai iya yin bayani akan abubuwan daya sani
B2 (upper intermediate)
Mutumin da yake da ƙwarewa ta B2 a harshe zai iya fahimtar maƙasudin abunda rubuce rubuce masu tsauri suke nufi, zai iya yin mu'amala sosai da mutanen da suke yin magana da harshen a matsayin harshen su na gado, zai iya yin anfani da wannan harshen domin yin rubuce rubuce masu ma'ana akan darussa da dama
C1 (Advanced English)
Mutumin da yake da ƙwarewa ta C1 a harshe zai iya fahimtar rubuce rubuce masu tarin yawa, kuma zai iya fahimtar magana koda ba'a fito ƙarara an bayyana abun da ake nufi ba. zai iya yin magana kai tsaye ba tare da inda inda ba, zai iya yin anfani da yaren yadda ya kamata a cikin jama'a, a ɓangaren ilimin dake buƙatar ƙwarewa, zai iya yin bayani da kyau a fannoni masu tsauri.
C2 (Proficiency)
Mutumin da yake da ƙwarewa ta C2 a harshe dai dai yake da mutumin da yake anfani da harshen a matsayin harshen gado kuma wanda ya karanci wannan harshen a makaranta don haka cikin sauƙi zai iya fahimtar duk abun da aka faɗa ko aka rubuta, zai iya taƙaita maganar da aka faɗa ko aka rubuta a gurare daban daban. Mutane 'yan tsiraru ne suke iya kaiwa wannan matakin muddin turancin bashi bane yaren su na gado
Zaka iya yin jarabawar Cambridge a wannan shafin domin sanin matakin ƙwarewar da kake da ita a turanci