Wasu daga cikin masu ziyartar wannan shafin ba ɗaliban makaranta bane, to amma suna da sha'awan ganin sun iya turanci.

An jima ana tambaya na cewa wai muna da wata makarantar koyan turanci ce domin manyan mutane?

To gaskiya babu wata makaranta da nake da ita ta koyan turanci a halin yanzu.

To amma me yasa kake neman wata makaranta bayan zaka iya yin karatu ta internet ba tare da malami ba?

Shin zai yiwu mutum yayi karatu ba tare da malami ba?

Wannan tambayar ta tuna min da lokacin da nake aji uku na makarantar firamare, duk da cewa na ƙware gurin rubutawa tare da karanta rubutun larabci, amma a lokacin bana iya karanta komai da turanci ko hausa sai dai sunana.

Mahaifiya ta ta kasance tana yawan karance karancen littafan adabin Hausa. Hakan yasa na kasance mai sha'awan ɗauko ire iren waɗannan littafan nan nata ina kallon hotunan dake ciki. sannu a hankali kuma na fara ƙoƙarin karanta abin da ke cikin wannan littafin. cikin ƙanƙanen lokaci naga na fara fahimtar wannan littafin, hakan yasa nima na kasance mai yawan ƙoƙarin karance karancen littafan adabin Hausa kamar mahaifiyata, ba tare da wani ya koya min yadda ake karatun Hausa ba. koda yake dai akwai wasu gyare gyare da mahaifiyata tayi mini kaman gurin haruffa masu lankwasa da kuma gurin karanta 'sh, ts, kw, ky, da kuma 'ƙy'

Ganin cewa na ƙware gurin karatun Hausa ba tare da malami ba, hakan yasa nayi amfani da hanyar dana bi gurin koyan karatun Hausa domin koyan karatun Turanci, kuma cikin ikon Allah na ƙware gurin karatun turanci ta hanyar yin karatu da kai na ba tare da malami ba

Sakamakon wannan nasara dana samu, hakan yasa na ɗauki ra'ayin cewa mutun zai iya koyan karatu ba tare da malami ba.

Ganin cewa ina karatun turanci ne galibi ba tare da ina sanin abin da nake karantawa ba, saboda rashin sanin ma'anonin kalmomin turancin, hakan yasa na koma ina sayen tare da karanta littafan Teach yourself (littafan koyan turanci cikin harshen hausa). Waɗannan littafan sun matuƙan taimaka min gurin sanin ma'anonin kalmomin turanci da dama.

Matsalolin da nake fama dasu gurin sanin ma'anonin kalmomi da grammar yazo ƙarke ne a lokacin ina JSS 1 bayan na mallaki ƙamus na turanci da Hausa wanda maɗaba'ar gaskiya ta Zaria ta buga. wanda a lokacin shine ƙamus na Hausa tilo da yake a kasuwa. sai kuma littafin New way of learning English wanda Kabiru Musa Jammaje ya wallafa, wanda kuma shima yake zama littafin koyan nahwun turanci cikin Hausa na farko.

Waɗannan littafan sun matuƙan taimaka min gurin ƙwarewa a turanci. koda yake bayan su na ci gaba da karanta wasu littafan kamar su Common mistakes in English, brighter grammar da kuma A'one English.

Sannan kuma yin mu'amala da mutanen da suka magana da turanci musamman a makaranta shima ya matuƙan taimaka min gurin gogewa a turanci.

Da ace lokacin na fara amfani da internet da kuwa abubuwa ma duk sun zo da sauƙi, to sai dai kash! ban fara amfani da internet ba sai a shekara ta 2008.

Don haka ka gode wa Allah da har kake iya karatu da kuma sanin yadda ake shiga duniyar gizo, don kuwa wannan ba ƙaramar kyauta bace Allah ya baka. Jahili a wannan zamanin shine wanda bai san internet ba, ba wai wanda bai yi karatu a makaranta ba.

Na koya ilimin lissafi da kaina

Tun lokacin da muka shiga darasin division a kimiyyar lissafi (mathematics), lissafi ya fara bani wahala, hakan yasa na dena mayar da hankali a duk lokacin da aka zo yi mana darasin lissafi, bisa zaton cewa ƙwaƙwalwata baza ta iya ɗaukan darasin lissafi ba. to sai dai wannan tinanin nawa ya sauya lokacin ina SSS 2, a sa'ilin da muke yin statistics, lokacin ne na fara fahimtar wannan darasin. Hakan yasa na koma ina karanta text books na mathematics tare da yin exercise na wannan littafin. a cikin watanni biyar kacal na ƙware a lissafin da yake ɗaukan wasu shekaru takwas. koda yake dai akwai wasu abubuwan da abokanai na suka nuna min a darasin mathematics waɗanda suka shige min duhu.

Na koyi coding (programming) da kai na

Wannan shafin nawa shine irin sa na farko da wani ɗan Naijeriya ya fara ƙirƙira, kuma har zuwa yau da nake rubuta wannan maƙala (21-6-2017), a kaf Nigeria babu irin wannan shafin, shekaru uku bayan ƙirƙirarsa. ni kaɗai na ƙirƙira wannan shafin ba tare da taimakon wani ba, ta hanyar amfani da programming language na PHP, HTML, Javascript da css. Mai yiwuwa zaka yi mamaki idan kasan cewa ban taɓa zuwa wata makarantar koyon computer ba. Duk na koya waɗannan coding ne a internet.

Na koya karatun Al-ƙur'ani da kaina

Na kasance na sauya makarantar Islamiyyar da nake zuwa, sai ya kasance wannan sabuwar makarantar dana koma sun yi mini nisa, domin kuwa sun kai har Suratul Maryam, sa'ilin dani kuma nake Suratul Muhammad. Hakan yasa na koma ina amfani da rediyo domin koyon sauran surorin da suka kuɓuce min kuma hakan ya yiwu.

Daga ƙarke.....

Maganar cewa wai lalle sai tare da malami ne ake iya karatu ba gaskiya bane, matuƙan dai mutum zai iya karanta abu ya kuma fahimta to lalle zai iya koyawa kansa karatu. da ace har wannan maganar gaskiya ce, to da kuwa ban iya ƙirƙirar wannan shafin ba yanzu haka. domin kuwa babu wanda ya taɓa koya mini komai akan harkar computer da internet. ni ne da kaina na koya a internet.

Kasancewar mutane da yawa ko kuma ƙwararrun masana suna gasgata wata magana, ba wai hakan yana nufin cewa wai lallai wannan maganar gaskiya bace, muddin babu wata hujja da zata tabbatar da wannan maganar, ilimi kogi ne, babu wanda zai ce wai ya kai maƙura a ilimi. A ɗabi'ance mutane sun kasance suna yin imani tare da yarda da duk wani ra'ayin da al'ummar yankin da aka haifo su suka yi imani dashi, koda kuwa wannan ra'ayin ba gaskiya bane. Shiyasa mutane biyu zasu iya tsintan kansu a lamari iri ɗaya ko kuma ka gaya musu magana iri ɗaya, amma kuma kowannen su zai iya yiwa wannan maganar ko lamarin fahimta iri daban, ba don komai ba sai don kowannen su ya fuskanci ƙalubale iri daban a rayuwa, don haka zai yiwa wannan lamarin fahimta ce a bisa mahanga ta masaniyar da yake da ita a rayuwa. misali idan mutum yana kudancin Nigeria, to akwai yuwuwar zai taso ne yana mai yin imani ɗari bisa ɗari da ra'ayoyin da al'ummar wannan yankin suka yi imani dashi, don haka zai taso yana mai yaƙinin cewa yawancin 'yan arewa jahilai ne kuma 'yan ta'adda, don haka duk inda yaga wani ɗan arewa kallon banza zai riƙa yi mashi, kuma wai shi a gurin shi ba wai ƙiyayya ko wulaƙanta 'yan arewa yake yi ba, a'a, wai shinan gaskiya yake faɗa. Amma kuma daga bisani bayan yazo arewan ya gane wa idanuwansa sai ya fahimci ashe wannan tunanin nashi duk ba gaskiya bane, to daga nan sai ya sauya tunani. Don haka yana da muhimmanci duk wani ra'ayi da iyayenka ko al'ummar yankin da kake suka gina ka akai kayi bincike akai domin tabbatar da gaskiyar shi. Domin rayuwa tana da abubuwa masu tarin yawa waɗanda zasu yiwu da kuma waɗanda baza su yuwu ba. Bazai yuwu ace mutum yasan komai ba, don haka a koda yaushe kasa a ranka cewa kaɗan ne daga cikin waɗannan abubuwan ka sani. Don kuwa akwai ra'ayoyi da labarai masu tarin yawa da muka yi imani dasu anan kasar hausa waɗanda daga bisani dana yi bincike akai na tabbatar da cewa ba gaskiya bane. Don ko ni nasha fama da iyayena lokacin da nake makarantar sakandare akan rashin zuwa makaranta kullum, bayan dana fahimci cewa ina da saurin fahimtar karatu idan na karanta littafi ba tare dama naje makarantar ba, sun ta neman su hana ni yin wannan karatun wai lalle sai dai na riƙa zuwa makaranta kullum, saboda su a tasu fahimtar babu yadda za'a yi mutumin da baya zuwa makaranta ya iya fahimtar karatun da ake yi a makaranta. Haka ma a lokacin dana ke gayawa abokanai na cewa ina koyon programming language nan ma fa kowa yana ta kashe min jiki, suna masu bani shawaran ai gwamma naje nayi diploma a computer school saboda Nigeria da certificate ne ake yin amfani kuma koda kuwa mutun yana da ilima amma bashi da certificate to wannan ilimin bashi da wani amfani. Amma kuma daga bisani dana nuna musu kuɗaɗen da nake samu ta internet yawancin waɗannan mutanen da suka ce karatun nawa bashi da wani amfani sune kuma suka dawo suna neman wai na koya musu yadda ake haɗa shafin internet da android apps.

Wani ƙarin misali kuma shine, a lokutan baya a nan ƙasar hausa mun kasance mun dogara ne akan makarantun zaure inda kowa ake biya masa karatunsa ɗaya bayan ɗaya, wanda hakan yake sawa mutum zai iya ɗaukan tsawan shekaru goma sha biyar kafin ya sauke ƙur'ani kawai, bama a batun sauran darussa. amma tun bayan da muka rungumi tsarin karatun da yake bada daman tara ɗalibai dukka a aji guda ana yi musu karatu lokaci guda, hakan yasa ilimin addini yanzu ya yawaita inda zaka samu yaro ɗan shekara goma sha guɗu ya sauke Al-ƙur'ani.

Amma kuma a lokutan baya yawancin mutane suna ganin cewa karatun zaure shine hanyar da tafi dacewa a koyi karatu.

Domin neman ƙarin bayani akan ɗabi'un mutane sai a duba ɓangaren psychology a manhaja ta ta ko kun san? wacce za'a iya yin downloading a play store

Aika Zuwa

Whatsapp

Home

© Copyright. Shamsuddeen Zakariya. All right reserved.