Difference between 'will' and 'would'

Babban banbancin dake tsakanin 'will' da kuma 'would' shine za'a iya yin amfani da 'would' a matsayin past tense amma shi 'will' baza a iya yin amfani dashi a past tense ba.

Yawancin masu koyon turanci suna rikicewa idan suka zo yin amfani da kalmar 'would'. Abun da yawanci yake rikitar da mutane shine ɗauka cewa a koda yaushe ana yin amfani da 'would' ne a matsayin 'past tense na 'will'. E gaskiya ne 'would' shine past tense na 'will', amma kuma ana yin amfani dashi a wasu lamurra da dama waɗanda basu da nasaba da past tense.

Yin am fani da kalmar verb a cikin jimla abu ne mai wahala koda kuwa kalmomi ne na asali waɗanda basa canzawa (regular verb). Akwai kalmomin verb na turanci da yawa waɗanda irregular verb ne, kuma dukkan regular verb da irregular verb suna da wasu irin tenses da zai yi wahala a iya haddacewa. Domin fahimtar banbancin 'would' da kuma 'will' yana da muhinmanci ka san yanayin da ake amfani dasu. Yanzu bari muyi bayani akan su.

Yadda ake yin amfani da 'Will'

  1. Ana yin amfani da 'will' domin bayyana abubuwan da muke da yaƙini akan su cewa zasu faru nan gaba.
  2. Amina will be in house. Amina zata kasance a gidan.

    We'll be there. zamu kasance a gurin.

  3. Zamu iya yin amfani da 'will' domin yin bayani akan abun da mutane suke son su yi ko abun da zasu iya yi
  4. We'll buy house this year. zamu sayi gida a wannan shekarar.

    Yusuf will likely join Army. akwai yuwuwar Yusuf zai shiga aikin soja.

  5. Zamu iya yin amfani da 'will' domin yin alƙawari
  6. I'll buy you a gift for your good performance. zan saya maka kyauta saboda ƙwazon ka.

    We'll go and visit our grandmother tomorrow. zamu je mu ziyarci kakarmu gobe.

  7. Zamu iya yin amfani da 'will' a conditional (kalmar dake nuna cewa abu zai yuwu ne kawai idan wani abu ya faru) domin faɗin abun da muke tunanin cewa zai faru a halin yanzu ko nan gaba
  8. I'll buy you a gift if you pass waec. zan siya maka kyauta idan ka ci jarabawar waec.

    You won't get job unless you have university degree. baza ka samu aiki ba face idan kana da digiri.

Yadda ake yin amfani da 'would'

  1. Zamu iya yin amfani da 'would you' ko 'would you mind', domin yin roƙo
  2. Would you buy me android phone, please? ko don Allah zaka saya mini wayar android?

    Would you mind staying at home? shin baza ka damu ba (idan aka buƙace ka) daka tsaya a gida?.

    Would you mind not going to market? shin rashin zuwa kasuwa bazai dame ka ba?.

  3. Zamu iya yin amfani da 'would you like' domin neman mutum ya amsa gayyatar mu ko buƙatar mu.
  4. Would you like soft drinks? ko zaka so (na kawo maka) lemun kwalba?

    Would you like to come school tomorrow? ko zaka zo makaranta gobe?

  5. Zamu iya yin amfani da 'I would rather' ko 'I'd rather' domin faɗin abun da muka fi so.
  6. I would rather buy smartphone, not laptop. na gwammace na sayi babbar waya ba na'urar laptop ba.

    I can't drink unclean water, i'd rather go home to get bottle water. bazan iya shan ruwa mara tsafta ba, na gwammace na je gida domin na samu ruwan kwalba.

  7. Zamu iya yin amfani da 'would' domin siffanta yadda muke tunanin kasancewar abu
  8. Women would look attractive with longer hair. dogon gashi zai yiwa mata kyau.

    Your parents would be happy if you buy them house. iyayen ka zasu yi farin ciki idan ka saya musu gida.

  9. Zamu iya yin amfani da 'would' domin bayyana sakamakon wani aiki.
  10. She burned the letters so that her husband would never read them. ta ƙona wasiƙun domin kada mijinta ya karanta su.
  11. Zamu iya yin amfani da would a 'second' da 'third conditional sentence'
  12. A turanci muna da conditional sentence guda uku. A first conditional muna yin amfani da 'will', amma a second conditional da third conditional zamu yi amfani ne da 'would'. Yanzu bari mu kawo misalai biyu.

    2nd conditional If i had five millions naira, i would built a house in Abuja. da ace ina da naira miliyan biyar da zan gina gida a Habuja.

    3rd conditional. I would never fell in love with her if i hadn't gone to Abuja. da ace ban je Habuja ba da kuwa bazan faya yin soyayya da ita ba

Aika Zuwa

Whatsapp

Home

© Copyright. Shamsuddeen Zakariya. All right reserved.