Zamantowa ƙwararre gurin rubutawa tare da yin magana da harshen turanci abu ne dake buƙatar bada himma da kuma ɗaukan lokaci mai tsawo.
Ɗalibai da yawa sukan rikice idan aka zo gurin yin amfani da kalmar 'are' da kuma 'were' a cikin jimla, don ko ni kaina na kasance wanda nake kasa banbance waɗannan kalmomin a lokutan baya.
Banbanci tsakanin 'are' da 'were'
Dukkaninsu 'are' da 'were' ana amfani dasu ne a cikin jimla idan 'subject' (mutumin daya kasance shine ya aikata wani aikin dake a cikin jimla) na wannan jimlar ya kasance jam'i ne (plural). Banbancin su kawai shine 'are' yana nufin present tense, shi kuma 'were' yana a mazaunin past tense ne.
Don haka tunda 'are' present tense ce, idan aka yi amfani da ita a cikin jimla hakan yana nufin jimlar ta zamanto present tense kenan.
Hakazalika tunda 'were' past tense ne; idan aka yi amfani dashi a cikin jimla hakan yana nufin jimlar ta kasance past tense kenan.
Misali:
The children are running around the pool. to anan gurin tun da anyi amfani da 'are' ne a maimakon 'were', to hakan yana nufin yaran suna kan yin guje guje kenan yanzun haka a kewayen kududdufin.
To amma idan kana so kace yaran sun yi guje guje ne a lokacin daya gabata, to anan sai kayi amfani da kalmar 'were', wato The children were running around the pool.
Abin lura
Duk da cewa da fari nace ana amfani da 'are' ko 'were' idan subject na wannan jimlar ya kasance jam'i ne, to amma duk da haka za'a iya yin amfani dashi a subject wanda yake ɗaukan ko yin aiki a matsayin singular ko plural. Misali kalmar 'You' tana ɗaukan singular ko plural. Wato tana nufin 'kai' ko 'ku'.
Misali:
'You are a good writer'. anan gurin fassarar wannan jimlar itace 'Kai ƙwararren marubuci ne'. Duk kuwa da cewa anyi amfani da kalmar 'are', hakan yana nufin a halin yanzu shi wannan mutumin ƙwararren marubuci ne a lokacin da ake yin wannan maganar. Amma idan aka yi amfani da kalmar 'were' wato 'You were a good writer.'; to hakan yana nufin dacan shi wannan mutumin ƙwararren marubuci ne amma banda yanzu.
A taƙaice de kalmomin 'are' da kuma 'were' jam'i ne na kalmar 'be' kuma ana amfani dasu ne a cikin jimla idan subject na wannan jimlar ya kasance plural ne. Banbancin su kawai shine 'are' ya kasance present tense ne. A yayin da kuma 'were' ya kasance past tense ne.
Aika Zuwa
© Copyright. Shamsuddeen Zakariya. All right reserved.