Vocabulary yana nufin kalmomin da akai amfani dasu a wajen rubuta wani harshe. Na rarraba wadannan kalmomi zuwa fanni dabam dabam domin yayi saukin fahimta. Kiyaye wadannan zai matukan taimakawa mai sha'awar koyan harshen turanci
Sassan Jikin Mutum
1. Head: Kai
2. Nose: Hanci
3. Mouth: Baki
4. Chest: Kirji
5. Finger: Yatsun hannu
6. Neck: Wuya
7. Eye: Ido
8. Shoulder: Kafada
9. Elbow: gwiwwan hannu
10. Hip: duwaiwai
11. Thigh: cinya
12. Knee: gwiywan kafa
13. Toes: yatsun kafa
14. Ankle: idan sahu
15. Foot: tafin kafa
16. Shin: kashin tsakiyan kafa
17. Hair: gashi
18. Forehead: goshin kai
19. Ear: kunne
20. Cheek: kumatu
21. Throat: makogwaro
22. Chin: habo
23. Lip: lebe
24. Nostril: kofar hanci
25. Face: fuska
26. Eyebrow: gira
27. Eyelashes: gashin saman ido
28. Teeth: hakora
29. Jaw: kashin fuska
30. Ribs: kasusuwan kirji
31. Pelvis: kashin kwankwaso
32. Brain: kwakwalwa
33. Stomach: tunbi
34. Kidney: koda
35. Intestine: hanji
36. Liver: hanta
37. Heart: zuciya
38. Lung: hunhu
39. Brain: kwanya
Sassan Jikin Dabba
1. Fang: fika, hakori mai tsini na kare ko damisa
2. Horn: kaho
3. Tail: bindi, jela
4. Hooves: kafaton dabba
5. Whisker: gashin bakin mage, damisa ko bera
Aikin Dakin Girki
1. Strain: tace abu da rariya
2. Sleve: tankade
3. Sprinkle: barbada abu misali barbada gishiri a abinci
4. Stir: gauraya abubuwa masu ruwa-ruwa
Saututtuka
1. Ring: karan kararrawa
2. Tick: kankanin kara irin karan motsin agogo
3. Crash: karan fashewa kamar fashewar gilashi
4. Rattle: karan kararrawa mai kacau-kacau
5. Sizzle: karan tuya
6. Hiss: karar faciwar iska daga kwallo ko tayar mota
7. Squeak: kukan bera
Aikace Aikacen Hannuwa
1. Clap: yin tafi
2. Pinch: tsinguli
3. Scratch: kankarewa ko susa
4. Stroke: shafa
5. Tickle: cakulculi
6. Point: nuni da hannu
7. Knock: kwankwasawa
8. Slap: mari
Aiki Da Jiki
1. Lift: daga abu sama
2. Carry: daukan abu
3. Hold: rike abu
4. Kneel: sanya gwiywa a kasa
5. Crouch: tsiguno
6. Lean: jingina
7. Drag: jan abu a kasa
8. Jump: tsalle
9. Push: turawa
10. Pull: janyowa
11. Climb: hawa abu
12. Drop: sakin abu
13. Fall: faduwa
14. Jog: gudu kadan kadan
15. Walk: tafiya
16. Sit: Zama
17. Throw: jefarwa
18. Punch: naushi
19. Catch: kamawa
20. March: yin maci
21. Raise: tashi sama
Sunan Ranaku
1. Sunday: lahadi
2. Monday: litinin
3. Tuesday: Talata
4. Wednesday:
5. Thursday: alhamis
6. Friday: Juma'a
Saturday: asabar
Sunayen Lokaci
1. Second: dakika daya
2. Minute: minti daya
3. Hour: sa'a
4. Day: rana daya
5. Week: sati daya
6. Month: wata daya
7. Year: shekara daya
8. Decade: shekaru goma
9. Century: karni (shekaru dari)
10. Millennium: shekaru dubu
Kalmomin Kasuwanci
1. Advertising: tallata haja
2. Travel: tafiye tafiye
3. Bank: banki
4. Contracts: kwantirati
5. Employment: daukan mutum aiki
6. Import: shigo da kaya daga kasar waje
7. Export: fitar da kaya zuwa kasar waje
8. Insurance: inshora
9. Market: kasuwa
10. Money: kudi
11. Property: kayayyaki daka mallaka
12. Sell: saidawa
13. Customer: abokin ciniki
14. Consumer: mai sayan kaya
15. Supply: yin odan kaya
16. Goods: kayayyaki
17. Demand: bukatan abu
Dabbobin Gida
1. Bull: sa
2. Cow: saniya
3. Calf: jaririn saniya
4. Dog: kare
5. Bitch: karya
6. Puppy: jaririn kare
7. Donkey: jaki
8. Sheep: tinkiya
9. Ram: rago
10. Colt: karamin doki
11. Lamb: jaririn tinkiya
12. Bee: kudan zuwa
13. Rabbit: zomo
14. Rat: bera
15. Parrot: aku
16. Spider: gizo-gizo
17. Snake: maciji
Launi
Red: Ja
orange: zuwan lemu
yellow: Ruwan dorawa
green: kore
blue: shudi
black: baki
pink
Brown: ruwan kasa
purple
'Ya'yan itatuwa
1. Apple: Wani irin yalo
2. Banana: Ayaba
3. Coconut: kwakwa
4. Lemon: lemun tsami
5. Mango: mangwaro
6. Orange: lemu
7. Pineapple: abarba
8. Tomato: timatir
9. Garlic: tafarnuwa
10. Onion: albasa