Home | About Us | Our Videos | Follow Us On Facebook

Download our Android app


Questions Tags

Lura da waɗannan misalan:
 1. You haven't ever went to Lagos, have you? baka taɓa zuwa Legas ba, ko ka taɓa zuwa?
 2. Your wife is five years younger than you, doesn't she? ka girma matarka da shekaru biyar, ko baka girme ta da waɗannan shekarun ba?
 3. Fatima can't speak Hausa, can she? Fatima baza ta iya yin magana da harshen Hausa ba, ko zata iya?

Za'a iya samar da question tags ne ta hanyar yin anfani da wasu kalmomi kamar 'have you?', 'doesn't she?', 'can't she?' da dai sauran su. Ana yin anfani da question tags ne domin sauya magana ta zamo tambaya, kuma mai maganar yana tsammanin cewa mai sauraro zai amince da abun da yake cewa.

Yadda ake samar da questions tags

In general, if the statement is positive, the question tag will be negative and vice versa. E.g

A bisa ƙa'ida, idan magana tana tabbatar da wani lamari ne, to question tag na wannan maganar zai kasance shi kuma yana yin inkari ne (musantawa). Misali: Your wife is five years younger than you (positive), doesn't she? (negative) wato "Ka girma matarka da shekaru biyar (wannan maganar tana tabbatar da abu ne), ko ba gaskiya bane? (wannan tambaya ce ta inkari)

Ƙarin misalai

 1. Jamila is a university graduate, isn't she? Jamila ta kammala karatun jami'a, ko bata kammala bane?
 2. He isn't the vice president, is he? bashi bane mataimakin shugaban ƙasa, ko shi ne?
 3. Police never killed anybody in the scene, have they? 'yan sanda basu kashe kowa a gurin ba, ko akwai wanda suka kashe?
 4. Your parents aren't going to live with you forever, are they? iyayenka baza su rayu har abada ba, ko kana ganin ba haka bane?
 5. Doctors are present when she delivered the baby, don't they? likitoci suna gurin lokacin data haifo jaririn, ko kuwa basa gurin?
 6. That was the type of phone i sold, wasn't it? wannan itace irin wayar dana sayar, ko ba ita bace?
 7. I don't need to study law in university, do i? babu buƙatar na koyi ilimin shari'a a jami'a, ko akwai buƙatar haka?
 8. He graduated from university this year, didn't he? ya kammala karatun jami'a a wannan shekarar, ko bai kammala ba?
 9. We were exhausting our data watching YouTube videos, weren't we? muna ƙarar da datan mu gurin kallon bidiyon YouTube, ko bama ƙararwa?
 10. They have exhausted their data on YouTube, haven't they? sun ƙarar da datan su gurin kallon YouTube, ko basu ƙarar ba?
 11. The computer didn't break, did it? kwamfutar bata fashe ba, ko ta fashe?
 12. She'll happy if you buy her computer, won't she? zata yi murna idan ka saya mata kwanfuta, ko baza tayi murna ba?
 13. We're no longer young, are we? yanzu mu ba yara bane, ko kana ganin har yanzu mu yara ne?
 14. Most people in Niger Republic can't speak English, can they? yawancin mutane a jamhuriyar Nijer baza su iya yin magana da turancin ingilishi ba, ko zasu iya?
 15. The university isn't in the north, is it? jami'ar ba a arewa take ba, ko a arewa take?
 16. You're not a university graduate, are you? kai ba wanda ya kammala karatun jami'a bane, ko kuwa?
 17. She can't speak good English, can she? baza ta iya yin magana da turanci sosai ba, ko zata iya?

Aika Zuwa

Whatsapp

Home

© Copyright 2014 & 2019 shamsuddeen inc. All right reserved.