Wasu ƙalubale da ɗalibai masu koyon turanci suke fama da ita itace kasa yin magana ko rubuta zance da harshen turanci duk kuwa da cewa zasu iya fahimtar maganar da wasu suke yi ko suke rubutawa da harshen turanci. Wannan matsalar na daga cikin wacce masu koyon turanci a wannan shafin suke yawan kawo mini ƙorafi.

To a taƙaice da akwai matakai biyu na koyon yare kamar haka
  1. Passive Skills
  2. Wannan shine matakin koyon yare ta hanyar sauraro da kallo da kuma ta hanyar karanta labarai ko wasu bayanai da aka rubuta da wannan yaren da kake son koya.
  3. Productive Skills
  4. Wannan shine koyon yare ta hanyar yin magana da yaren da kake son koya ko kuma ta hanyar rubuta zance a takadda ko wani abun rubutu.
Muddin mutum ya kasance yana kallo da sauraron masu magana da turanci ko karanta rubuce rubucen turanci ne kawai amma baya gwada yin magana da turancin ko rubata zance da turancin to lalle abubuwan da yake koya kawai zai iya, wato koyon yadda ake fahimtar masu magana da turanci ko koyon yadda ake fahimtar maganar da aka rubuta da turanci. Amma kuwa bazai iya yin magana da turanci ko rubuta magana da harshen turanci ba tunda ba waɗannan bane abubuwan da yake koya

Idan har mutum yana fahimtar abun da mutane suke cewa ko suka rubuta da wani yare amma kuma bazai iya yin magana da wannan yaren ba ko rubuta zance da wannan yaren to ina da yaƙinin cewa yana bin matakin farko ne kawai (sauraro, kallo ko karanta labari) amma baya bin mataki na biyu (wato yin magana da yaren ko rubuta shi).

E, gaskiya ne matakin koyon karatu na productive skill (wato yin magana da yare ko rubutashi) yana da wahala, shi yasa yawancin mutane suka fi bin matakin koyon karatu na passive skill (wato sauraro ko karantawa) domin shine matakin koyon yare mafi sauƙi, hakan shi yasa zaka ga mutum yayi karatu har zuwa jami'a amma bazai iya yi maka magana da turancin ba duk kuwa da cewa zai iya fahimtar duk abun da ake cewa da turancin. Shawarar da zan ba masu fama da irin wannan matsalar itace su riƙa ƙoƙarin gwada yin magana ko rubata zance cikin harshen turanci ba wai kawai su mayar da hankali gurin sauraron masu magana da turanci, kallon fina finai da kuma karance karance ba. Na san cewa mutane suna jin kunya gurin yin magana da wani yare idan basu ƙware ba domin gudun kada ayi musu dariya, domin kyaucewa wannan matsalar, sai ka fara koyon yin magana da turancin a zuciya idan ka samu guri ka natsu ko ta hanyar rubuta zance a littafi ko text editor na wayar ka, daga bisani idan ka fara ƙwarewa sai ka koma kana yin chatting a social media, daga bisani kuma idan ka samu ƙwarewa zaka iya yin magana da yaren ba tare da zullumi ba.

Ni kaina nayi fama da irin wannan matsalar a shekarun baya, idan akwai masu bibiya na a shekarun baya lokacin da nake da shafin internet na blog kafin na buɗe wannan shafin, zaku fahimci cewa turancin da nake yin amfani dashi da fari a wancan lokacin akwai rashin ƙwarewa sosai a cikin shi, amma kuma albarkin yawan rubuce rubucen zantuka da nake yi cikin harshen turancin ba tare da jin kunya ba yasa na goge sosai a turanci, ba wai rubutawa ba harma da yin magana da turancin. muddin mutum ya iya rubuta zance da turanci to ɗaya suke da yin magana da turancin da baki, sai dai mai yuwuwa zai iya samun matsala gurin furta wasu kalmomin, domin magance wannan matsalar sai mutum ya riƙa yin amfani da fasahar TTS domin sauraron yadda ake furta kalmar da bai san yadda ake furtata ba.

Aika Zuwa

Whatsapp

Home

© Copyright. Shamsuddeen Zakariya. All right reserved.