Rubutun wasiƙa ya kasu zuwa kashi uku
  1. Formal letter (wasiƙar ban girma)
  2. Informal letter (wasiƙa wacce bata ban girma ba)
  3. Semi formal letter (wasiƙa wacce wani sashi nata na bangirma ne)

This is business or official letter, such as employment letters, letters of complaints, letters to editors of newspapers and magazines e.t.c.

Formal letter wasiƙa ce ta kasuwanci ko ta hukuma, wasiƙun yin ƙorafi, wasiƙu zuwa ga mawallafan jaridu da mujallu da dai sauransu.

The structure and nature of a formal letter (tsari da kuma fasalin rubuta formal letter)

1. THE WRITERS ADDRESS:

This is written at the top right hand. The senders address does not carry his/her name at the top. Punctuation marks in the address is optional. Date is the last item on the address including the day and month, which should be separated from the year with a comma.

1. ADIRESHIN MAI RUBUTU: Ana rubuta adireshin mai rubutunne a sama daga hannun dama. sannan ba'a sanya sunan wanda ya aiko da wasiƙar a cikin adireshin. Ba dole bane sai anyi anfani da punctuation mark a cikin rubutun adireshin. Kwanan wata shine abu na ƙarke a adireshin, wanda ya ƙunshi rana da wata, waɗanda za'a raba su da shekarar ta hanyar amfani da comma

2 RECIPIENT'S ADDRESS

This is the address of the person to whom you're writing the letter. It is written at the left hand, below the writer's address. The recipient's address carries neither date nor the recipient personal name.

ADIRESHIN WANDA AKA AIKO MA WASIƘAR

Wannan shine adireshin mutumin da kake rubutawa wasiƙar, ana rubutashi ne a hannun dama ƙasa da adireshin mai rubutu. Ba'a sanya kwanan wata haɗe da adireshin wanda za'a aika wa saƙon sannan ba'a sanya sunan shi.

3 THE SALUTATION (KALMAR GIRMAMAWA)

Salutation is written after the recipient's address, the most common are "Dear sir' for a male recipient. and "Dear Madam" for a woman. The first letters of the words in the salutation are usually in capital letters. Other forms of salutation are your Excellency (for presidents, governors and ambassadors)

Ana rubuta kalmar girmamawa a gaban adireshin wanda za'a aikawa wasiƙar. kalmomin girmamawa waɗanda aka fi sani sune kamar haka "Dear sir" (ana anfani da wannan ne kawai ga maza), sai "Dear Madam" (ana anfani da wannan ne kawai ga mata). Harafin farko na kalmar girmamawan dole ya kasance babban harafi ne. Wasu kuma kalmomin girmamawa da ake amfani dasu sune "your excellency" (ana amfani da shine kawai ga shuwagabannin ƙasa, gwamnoni da jakadu)

4. THE TITLE OF THE LETTER (ABUN DA WASIƘAR TA ƘUNSA)

It give more details regarding the context of the letter, it should be short and underline, if however all the letters are in capital letters, it should not be underlined.

Yana yin ƙarin bayani ne akan abun dake cikin wasiƙar. Yana da kyau ya kasance mara tsawo kuma sannan a ja layi a ƙasa idan anyi anfani da ƙananun haruffa ne, amma baza a ja layi ba idan anyi anfani da manyan haruffa.

5. THE SUBSCRIPTION (KALMOMIN HAZA WASSALAM)

This is "yours faithfully" with the writer's signature on the next line, then followed by his name and surname.

Wannan shine "yours faithfully" tare da sa hannun mai rubutun a layin ƙasa, sannan sai sunan shi da sunan baban shi.

Wannan rubutun na ƙasa shine misalin formal letter.

Box 59, Sabon Gari L.G.A. Kano State
8 March 2019


The general manager Albabello Trading company.
No. 50 Sabon Gari Main Market, Zaria, Kaduna State.
    APPLICATION FOR THE POST A SUPERVISOR
In response to your advertisement in the AdSense online advert, i hereby apply for the post of a supervisor in your company. My name is Ibrahim Abdul-kadir. I am from Sabon Gari of Kano state. I attended central school, Sabon Gari where i obtained my first school leaving certificate. And M.T. Ibrahim college Kano where i got my west African School certificate (WASC). Before i was admitted to the federal university of technology Kano, where i graduated as a Civil Enginear with a second class upper, i obtained my National Diploma (ND) from Nuhu Bamalli Polytechnic Zaria. In the same profession. I have a year and ten month's experience during my industrial training (IT), With Reynold construction company, kano branch.
Enclosed are the photocopies of my credentials and reference letters from the personnel manager of Reynold construction company (RCC) at each end of my three respective industrial trainings.
I will be very grateful if my application is positively considered.


Yours faithfully
(signature here)
Ibrahim Abdul-kadir

Is a letter you can write to people whom you feel free to tell anything" about your life, e.g letter to close friends, relative, classmates, colleagues. e.t.c.

Informal letter wasiƙa ce da zaka iya rubutawa zuwa ga mutanen da kake jin zaka iya gaya musu komai, misali abokane na ƙud da ƙud, dangi, abokanen karatu ko abokanen aiki.

STRUCTURE OF INFORMAL LETTER (tsarin yanda ake rubuta informal letter)

1. The writer's address with date: should be at the top right hand, if the letter is going abroad, the writer's country should be indicated.

Adireshin mai rubutun da kwanan wata zai kasance ne a sama daga hannun dama. Idan za'a aika da wasiƙar ƙasar waje ce, to akwai buƙatar mai rubuta wannan wasiƙar ya rubuta sunan ƙasar shi.

2. Salutation: The recipient's name, especially if he is a friend should be mention. e.g. "Dear Yusuf" if however, the recipient is an elder or a parent, we may not mention their name, but what he/she is to us, eg dear mother, dear father, dear brother or dear sister e.t.c. You can use slang, proverb or native words.

2. Kalmar girmamawa: Ana buƙatar a anbaci sunan wanda za'a aikawa saƙƙon, musamman idan aboki ne, Misali "dear Yusuf", amma idan wanda za'a aikawa saƙon wani babba ne ko iyaye, to anan baza mu anbaci sunan su ba, sai dai zamu yi anfani da sunan matsayin da suke a gurin mu, misali "Dear mother" (zuwa ga mama), "Dear father" (zuwa ga baba), "Dear brother" (zuwa ga yaya) da dai sauransu. zaku iya yin amfani da wasu kalmomi waɗanda ba karɓaɓɓu ba ko kuma yin anfani da karin magana.

Wannan rubutun na ƙasa shine misalin informal letter

No. 11 Lagos Street Sabon Gari Zaria Kaduna State
7 March 2019


Dear Abdurrahman.
"O my friend, you are worry oh! However, i can't wait again, i have decided to bridge the gap. Abdurrahman, I want to inform you that we shall be coming home this Sallah season. So, prepare to take me to some important Walimah, and to introduce me to correct guys.
    My regards to your Mum, Dad and the big bros.
Lots of love, Shamsuddeen

This is letter we write to people who deserve some measured of respect from us because of their age, position or their role in the society. Such people include our school heads, teacher, lecturers and Imams.

Semi formal letter wasiƙa ce da muke rubutawa zuwa ga mutane da muke musu kallon mutunci saboda shekarunsu, matsayinsu ko matsayin da suke dashi ga al'umma. Irin waɗannan mutanen sune kamar shuwagabannin makarantu, malamai, malaman jami'a da kuma limamai.

STRUCTURE OF SEMI FORMAL LETTERS (Tsarin yadda ake rubuta semi formal letters)

1. The tone and use of the language is formal; because the recipient are not our age mates. For example, you can't say "what's up'.

Irin kalaman da zaka yi anfani dasu Dole ya kasance akwai girmamawa da ladabi a ciki, saboda wanda zaka aikawa saƙon ba sa'anka bane, Misali baza ka iya cewa "ya take ne" ba.

2. It has only one address, which is the address of the writer, like informal letter; the address should be written at the top right hand.

Adireshi guda ɗaya ake sa mata, wato adireshin mai rubutun, kamar dai informal letter; ana buƙatar a rubuta adireshin daga sama a hannun dama.

3. The respect in the tone of the letter is also reflected on the salutation.

lafazin girmamawar da zaka yi anfani dasu zai kasance ya dace da kalmomin girmamawan da ake anfani dasu a cikin wasiƙar.

The complimentary close could be "yours sincerely" followed by either the writer's full name or initial and surname. And there is no signature.

Kalmar girmamawa ta rufewa da ake anfani da ita itace "yours sincerely", sannan daga bisani a sanya cikakken sunan marubucin wasiƙar, sunan shi na tsakiya ko sunan mahaifin shi.

Wannan wasiƙar ta ƙasa itace misalin semi-formal letter

No. 11 Mamman Daku Street Sabon Gari Zaria Kaduna State
7 March 2019


Dear Brother Umar I'm writing to formally invite you to be a representer at the upcoming conference. The topic of this conference is "Unity" The conference will be held in Zaria Hotel on March 5 2019. For your information, Professor Ango Abdullahi of ABU University will be the opening keynote speaker. I would be glad if you can contribute to this prestigious conference. I'd appreciate it if you could kindly reply soon. From there, I can provide you with any further information you may require.

Your sincerely Yusus M. Bala


Aika Zuwa

Whatsapp

Home

© Copyright. Shamsuddeen Zakariya. All right reserved.