Direct and Indirect Speech Koyon Turanci Da Hausa

Essay

Essay can be defined as a short piece of writing on a particular subject, especially one done by students as part of the work for a course.

Abun da essay yake nufi shine wani gajeren rubutu akan wani darasi, musammam darasin da ɗalibai zasu yi akan wani darasi da suke karanta.

Types of Essay

  1. Exposition
  2. Narration
  3. Description
  4. Argument
  1. Exposition
  2. This is an informative and short piece of writing that provide clear information and explanation on a particular subject. This type of essay involved explaining a topic using good information, facts and clear examples.

    Exposition wani nau'in rubutu ne mai ilmantarwa wanda yake yin bayani akan wani darasi. Mutumin da yake rubuta exposition essay zai kasance yana mai amfani da hujjoji da kuma misalai masu ilmantarwa akan darasin.

  3. Narrative essay/narration
  4. This is where the writer tells real life experience story, such as biographies, short stories e.t.c.

    Narrative essay wani salon rubutu ne inda mai rubutun yake yin bayani akan labarai waɗanda suka faru da gaske, kamar tarihin rayuwa ko gajerun labarai da dai sauransu.

  5. Descriptive Essay/Description
  6. This is giving a clear description of person, place, object or event.

    Descriptive essay wani salon rubutu ne da ya ƙunshi bada gamsashshen bayani akan mutum, wani guri, wani abu ko wani lamari.

  7. Argumentation/Argumentative essay
  8. Argumentation essay is a form of essay in which a writer persuades his audience through logic, facts and evidence to accept his point of view or recommendations.

    Argumentative essay wani nau'in salon rubutu ne inda mai rubutun zai zaburar da masu karatu ta hanyar amfani da hujjoji domin su amince da ra'ayi ko shawarwarinsa.

Aika Zuwa

Whatsapp

Home

© Copyright. Shamsuddeen Zakariya. All right reserved.