Concord is a situation in which the words in a sentence match each other according to the rules of the grammar.

Concord shine yanayin da kalmomin dake cikin jimla suke dacewa da juna bisa ga ƙa'idojin nahawu.

Subject or verb concord

This shows that if subject is singular, the verb must be singular too. And when the subject in the sentence is plural, the verb must be plural also.

subject or verb concord yana nuna cewa idan har subject (mutumin daya aikata aiki) na wata jimla ya kasance "singular" ne, to kalmar aikin dake cikin wannan jimlar itama dole zata kasance "singular". Hakama idan subject na wannan jimlar "plural" ne, to anan ma "verb" (kalmar aiki na wannan jimlar) shima zai kasance plural ne. Misali:

Ibrahim likes to play football. Ibrahim yana son buga ƙwallon ƙafa.

A wannan jimlar tunda subject na wannan jimlar (Ibrahim) third person singular ne, to dole kalmar verb data biyo bayan wannan kalmar ta kasance an sa mata "s". ku duba gurin person domin ƙarin bayani.

Amina and Maryam like to play football. Amina da Maryam suna son buga ƙwallon ƙafa.

A wannan jimlar tunda subject na wannan jimlar (Amina and Maryam) third person plural ne, to anan gurin baza a sanya "s" a gaban kalmar aikin data biyo baya ba.

She is very smart girl. ita yarinya ce mai matuƙar ƙwazo.

Anan gurin tunda subject na wannan jimlar (she) ya kasance singular ne, to dole object na wannan jimlar (girl) shima ya kasance yana singular.

They are very smart girls. su 'yan mata ne masu ƙwazo.

Anan tunda subject na wannan jimlar (they) ya kasance 'plural' ne, to dole 'object' na wannan jimlar (girls) shima ya kasance 'plural' ne.

Aika Zuwa

Whatsapp

Home

© Copyright. Shamsuddeen Zakariya. All right reserved.