Home | About Us | Contact Us | Follow Us On Facebook

Jarabawa ta objectives akan darasin Prefix And Suffix

Ana bukatar ku zabi amsar data dace sannan ku latsa maballin 'Submit Exam' domin ganin sakamako

Ana yin anfani da prefix da kuma suffix ne a farko ko a karshen kalma domin samad da kalma daga cikin wata kalmar. Ana bukatar ku gwada kwarewarku akan darasin prefix da kuma suffix ta hanyar amsa wadannan tambayoyin.

1. Tambaya ta farko: a wani aji haruffan 'co-' suke (shin prefix ne ko suffix)?

haruffan 'co' suna ajin prefix ne, ana sanya su a farkon kalma kuma suna nufin 'company'
haruffan 'co' suna ajin suffix ne, ana sanya su a karshen kalma kuma suna nufin 'company' ne
haruffan 'co-' suna ajin prefix ne, ana sanya su a farkon kalma kuma suna nufin 'cooperate' (wato abubuwa dake aiki tare)

2. Tambaya ta biyu: 'A wani aji haruffan 'sub-' suke, kuma idan aka sanya su a kalma me suke nufi?

'sub-' suna ajin suffix ne kuma akan sanya su a karshen kalma, kuma suna nufin 'submit'
haruffan 'sub-' suna ajin prefix ne; akan sanya su a farkon kalma, kuma suna nufin 'abun dake cikin wani abun'
haruffan 'sub-' suna ajin suffix ne, ana sanya su a karshen kalma kuma suna nufin 'abun dake cikin wani abun'

3. Tambaya ta uku: 'a wani aji haruffan 're-' suke kuma idan aka sanya su a kalma me suke nufi?'

haruffan 're' suna ajin prefix ne, ana sanya su a farkon kalma, kuma suna nufin 'sake maimaitawa'
haruffan 're' suna ajin prefix ne, akan sanya su a farkon kalma kuma suna nufin 'read' (wato karanta)
haruffan 're-' suna ajin suffix ne, akan sanya su a karshen kalma kuma suna nufin 'sake maimaitawa'

4. Tambaya ta hudu: a wani aji haruffan 'ability' suke, kuma idan aka sanya su a kalma me suke nufi?.

haruffan 'ability' suna ajin suffix ne, akan sanya su a karshen kalma, kuma suna nufin 'mai yiwuwa'
haruffan 'ability' suna ajin prefix ne, akan sanya su a karshen kalma kuma suna nufin 'mai yuwuwa'
haruffan 'ability' suna ajin prefix ne, akan sanya su a farkon kalma, kuma suna nufin 'mai yiwuwa'

5. Tambaya ta biyar: a wani aji haruffan '-ation' suke kuma idan aka sanya su a kalma me suke nufi?

haruffan '-ation' suna ajin prefix ne, ana sanya su a karshen kalma kuma ana anfani dasu ne domin samar da suna daga cikin kalmar aiki (makes nouns from verbs)
haruffan '-ation' suna ajin suffix ne, ana sanya su a farkon kalma kuma ana anfani dasu domin samar da siffa daga cikin kalmar aiki (makes adjectives from verbs)
haruffan '-ation' suna ajin suffix ne, ana sanya su a karshen kalma domin samar da suna daga cikin aiki (makes nouns from verbs)

6. Tambaya ta Shida: a wani aji haruffan '-able' suke kuma me suke nufi idan aka sanya su a kalma?

haruffan '-able' suna ajin suffix ne, ana sanya su a karshen kalma kuma suna nufin 'abu mai yiwuwa'
haruffan '-able' suna ajin prefix ne, ana sanya su a karshen kalma kuma suna nufin 'abu mai yiwuwa'
haruffan '-able' suna ajin suffix ne, ana sanya su a farkon kalma kuma suna nufin 'mai yiwuwa'

Aika Zuwa

Facebook Twitter Whatsapp

Home© Copyright 2014 shamsuddeen inc. All right reserved.