Home | About Us | Contact Us | Follow Us On Facebook

Jarabawa ta objectives akan darasin Miscellaneous

Ana bukatar ku zabi amsar data dace sannan ku latsa maballin 'Submit Exam' domin ganin sakamako

1. Tambaya ta farko: Me kalmar 'verb' take nufi?

kalmar verb tana nufin 'siffa'
Kalmar verb tana nufin 'kalmar aiki'
Kalmar verb tana nufin 'suna'

2. Tambaya ta biyu: me kalmar 'adjective' take nufi?

kalmar adjective tana nufin 'siffa'
kalmar adjective tana nufin 'kalmar aiki'
kalmar adjective tana nufin 'suna'

3. Tambaya ta uku: 'me kalmar Antonyms take nufi?'

kalmar antonyms sune kalmomi masu ma'ana iri guda
kalmar antonyms sune kalmomin da ake rubutasu yanayi guda, to amma kuma suna daukan ma'anoni mabambamta
kalmomi kishiyoyin juna sune ake kira antonyms

4. A fannin nahawun turanci, kalmar article sune 'the, an da kuma a, tambaya anan itace, yaya ake anfani da harafin 'a' ko kalmar 'the'?.

ana anfani da 'a' ko 'the' ne kawai idan kalmar da zata biyo bayanshi ta fara da wasali ne
ana anfani da 'a' ko 'the' ne kawai idan kalmar da zata biyo bayanshi ta fara da harafi ne.
ana anfani da 'a' ko 'the' ne kawai idan kalmar da zata biyo bayanshi ta fara da kalmar aiki ce

5. Tambaya ta biyar: a wasu lokutan ana anfani da 'an' a maimakon 'a', a wani irin yanayi ne hakan ke faruwa?

idan kalmar da zata biyo bayanshi ta fara da wasali ne ko harafin 'h' da ake furtata kamar yadda ake furta harafin 'a'
idan kalmar da zata biyo bayanshi ta fara da harafi ne, sannan kuma wasali ne ya biyo bayan harafin
idan kalmar da zata biyo bayanshi ta fara da 'an' ne

6. Tambaya ta Shida: Capital letters yana nufin manyan haruffa, tambaya anan itace, a ina ake anfani da capital letters?

 1. ana anfani da capital letters a duk harafin farkon sunan mutum
 2. ana anfani da capital letters a duk harafin farkon sunan wani gari.
 3. ana anfani da capital letters a duk harafin farkon sunan littafi mai tsarki.
 4. ana anfani da capital letters domin banbance sunan Ubangiji mahalicci da kuma abin da wasu suke bautawa wanda ba Allah ba.
 5. ana anfani da capital letters a duk farkon wata jimla.
 6. Ana anfani da capital letters a duk harafin farko na sunan ranaku ko watanni
 7. ana anfani da capital letter a duk harafin farkon sunan addini.

 1. ana anfani da capital letter a duk harafin farko na sunan kayayyakin lantarki.
 2. ana anfani da capital letter a duk harafin farkon sunan kayayyakin hada mota.
 3. ana anfani da capital letter ne a duk harafin farko na sunan kayan girki.

 1. ana anfani da capital letters a duk harafin farkon sunan abinci
 2. ana anfani da capital letter a duk harafin farkon sunan motoci.
 3. ana anfani da capital letter a duk harafin farko na sunan kayan marmari
 4. ana anfani da capital letter a duk harafin farko na sunan bishiyoyi.
 5. ana anfani da capital letter a duk harafin farko na sunan kayayyakin abinci.

Aika Zuwa

Facebook Twitter Whatsapp

Home© Copyright 2014 shamsuddeen inc. All right reserved.