1. Idan za'a bincika kalma indai har ana buƙatar kalmar ta fito a sakamakon bincike to a tabbatar ana yin amfani da haruffan Hausa masu lanƙwasa a guraren daya kamata ayi amfani da dasu. Idan wayarka bata ɗauke da haruffan Hausa to ka shiga play store kayi install wannan app mai suna Switch Keyboard a wayarka wanda zai baka damar yin amfani da haruffan Hausa dama na turanci.
2. Idan za'a bincika kalma, indai har ana buƙatar kalmar ta fito a sakamakon bincike, to zaifi dacewa kada a sanya 'plural', Wato kalmomin da suke ɗauke da harafin 's' ko 'es' a ƙarshensu, wandanda ake sanyawa domin maida kalma jam'i. Misali, 'boy' da kuma 'boys', 'box' da kuma 'boxes'. Zaifi dacewa ku bincika 'boy' ko 'box' ne kawai don idan kun sanya 'boys' ko 'boxes' baza ku samu sakamako ba
3. Idan za'a bincika kalma, indai har ana buƙatar kalmar ta fito a sakamakon bincike, to zaifi dacewa kada a bincika kalma mai ɗauke da 'past participle'. Wato kalmar dake ɗauke da haruffan 'ed' ko 'd' a ƙarshenta wanda ake anfani dasu domin nuna cewa kalmar tana 'past tense'. Misali kalmar 'look' (present tense) da kuma 'looked' (past tense), zaifi dacewa ku bincika 'look' domin idan kun bincika 'looked' baza ku sami sakamako ba. Koda dai a wasu lokutan mukan sanya kalmomi masu dauke da 'past participle' amma dai basu da yawa sosai
4. Idan za'a bincika kalma, indai har ana buƙatar kalmar ta fito a sakamakon bincike, to zaifi dacewa kada a bincika 'comparative' ko 'superlative' na 'adjectives', misali kalmar 'high' (tsayi), 'higher' (matsakaici) da kuma 'highest' (mafi tsayi). Zaifi dacewa ka bincika 'high' ne kawai domin idan ka bincika 'higher' ko 'highest' baza ka samu sakamako ba5. Idan za'a bincika kalma idan har ana buƙatar kalmar ta fito a sakamakon bincike, to zaifi dacewa kada a bincika kalmomi masu ɗauke da 'present perticiple', wato kalmomin da ake samar dasu ta hanyar sanya haruffan 'ing' a ƙarshen kalma. Misali kalmar 'going' wacce aka samad da ita daga cikin kalmar 'go'
6. Idan za'a bincika kalma zaifi dacewa kada a bincika kalma mai ɗauke da 'prefix', ko 'suffix' misali 'like' da kuma 'unlike' sai kuma 'mathematics' da 'mathematically', zaifi dacewa a bincika 'like' ne ko 'mathematic' kawai domin mai yiwuwa idan an bincika 'unlike' ko 'mathematically' baza a sami sakamako ba. To amma saboda muhimmancin da ire iren waɗannan kalmomin suke dashi musamman ga masu koyon turanci; akwai kalmomi da yawa da suke ɗauke da 'prefix' da 'suffix' waɗanda muka sanya a cikin wannan ƙamus din. yana da muhimmanci kusan asalin kalmomi domin muddin mutum ya gane asalin kalma to zai iya gane ma'anar dangoginta. Domin neman ƙarin bayani akan wannan to duba shafin 'Tambayoyin da aka saba yi'
7. Wannan shafin ba 'online translator' bane, wato ba wanda zai iya fassara 'sentence' (cikakkiyar jimla) bane, a'a anyi shine musamman domin fassarar 'word' (kalma) ko 'phrase' (kalmomi biyu a hade) misali "family" (=word) da kuma "family planning" (= phrase). don haka duk wani yunƙuri na fassara cikakkiyar jimla zai bada sakamakwan 'error' ne kawai.
Kamus.com.ng is an online/offline English to Hausa And Hausa to English comprehensive bilingual Dictionary (or Kamus in Hausa) containing thousands of British and American English words/phrases and Abbreviations.
The website/app provide definition of any existing English or Hausa word and phrase.
Each words came along with parts of speech.
We included hausa descriptions of complex and ambiguous definitions
We specified British Audio and IPA pronunciation of any English word for those wishing to know how to pronounce a particular word.
We provide English & Hausa bilingual usage sentences, description images, audio pronunciations of all Hausa words, pluralization of Hausa words, and origins of Hausa words derived from Arabic or English.
However this website came along with English to Hausa learning resources designed specifically for native Hausa wishing to learn English as second language.
Scientific words, medical words, geology, geography, biology, anatomy, chemistry, physics, literature, computing, psychology and linguistics words were included and precisely translated to Hausa.
Enjoy your stay here and also contribute to its growth by linking to us or inform others about this website.
The dictionary is frequently being updated and it works both online and offline.
If there is any missing word in the dictionary please send us the word and we'll add the word as soon as possible