Koyon Turanci Da Hausa


Home | About Us | Contact Us | Follow Us On Facebook


Turancin English yare ne mai matukan wahala, amma duk da haka kuma yare ne mai matukan ban sha'awa. Ba wai mu masu koyon wannan yaren a matsayin harshen kasar waje ba; koda ma mutanen da suke anfani da wannan yaren a matsayin harshen gado sukan tafka kurakurai a wasu lokutan.

Zamantowa kwararre gurin rubutawa tare da yin magana da harshen turanci abu ne dake bukatar bada himma da kuma daukan lokaci mai tsawo.

Dalibai da yawa sukan rikice idan aka zo gurin yin anfani da kalmar 'are' da kuma 'were' a cikin jimla, don ko ni kaina na kasance wanda nake kasa banbance wadannan kalmomin a lokutan baya.

Banbanci tsakanin 'are' da 'were'

Dukkaninsu 'are' da 'were' ana anfani dasu ne a cikin jimla idan 'subject' (mutumin daya kasance shine ya aikata wani aikin dake a cikin jimla) na wannan jimlar ya kasance jam'i ne (plural). Banbancin su kawai shine 'are' yana nufin present tense, shi kuma 'were' yana a mazaunin past tense ne.

Don haka tunda 'are' present tense ce, idan aka yi anfani da ita a cikin jimla hakan yana nufin jimlar ta zamanto present tense kenan.
Hakazalika tunda 'were' past tense ne; idan aka yi anfani dashi a cikin jimla hakan yana nufin jimlar ta kasance past tense kenan.

Misali:
The children are running around the pool. to anan gurin tun da anyi anfani da 'are' ne a maimakon 'were', to hakan yana nufin yaran suna kan yin guje guje kenan yanzun haka a kewayen kududdufin.

To amma idan kana so kace yaran sun yi guje guje ne a lokacin daya gabata, to anan sai kayi anfani da kalmar 'were', wato The children were running around the pool.

Abin lura
Duk da cewa da fari nace ana anfani da 'are' ko 'were' idan subject na wannan jimlar ya kasance jam'i ne, to amma duk da haka za'a iya yin anfani dashi a subject wanda yake daukan ko yin aiki a matsayin singular ko plural. Misali kalmar 'You' tana daukan singular ko plural. Wato tana nufin 'kai' ko 'ku'.

Misali:
'You are a good writer'. anan gurin fassarar wannan jimlar itace 'Kai kwararren marubuci ne'. Duk kuma da cewa anyi anfani da kalmar 'are', hakan yana nufin a halin yanzu shi wannan mutumin kwararren marubuci ne a lokacin da ake yin wannan maganar. Amma idan aka yi anfani da kalmar 'were' wato 'You were a good writer.'; to hakan yana nufin dacan shi wannan mutumin kwararren marubuci ne amma banda yanzu.

A takaice de kalmomin 'are' da kuma 'were' jam'i ne na kalmar 'be' kuma ana anfani dasu ne a cikin jimla idan subject na wannan jimlar ya kasance plural ne. Banbancin su kawai shine 'are' ya kasance present tense ne. A yayin da kuma 'were' ya kasance past tense ne.

Aika Zuwa

Facebook Twitter Whatsapp

Home

© Copyright 2014 shamsuddeen inc. All right reserved.