Home | About Us | Contact Us | Follow Us On Facebook


Tenses yana nuni ne ga lokacin gudanad da wani aiki. Akwai tenses da yawa amma a wannan shafin zamu duba guda Uku ne kawai (simple present tense, present continuous tense da kuma past tense) sannan kuma daga karshe mu kawo misalan guda uku, wato present tense, past tense da kuma past perfect tenses.

 1. Simple Present tense:
 2. Ana anfani da simple present tense ne domin nuna cewa aikin yana faruwa yau da kullum (koda yaushe). Jimlar da za'a iya anfani da ita zata iya kasancewa positive (jimlar da take tabbatar da magana), za kuma ta iya kasancewa negative (jimlar da take musanta magana) ko kuma question (jimla ta tambaya)

  Misali

   I take the book to the office. Ina kai littafin zuwa ofishin.

   Do i take the book to the office. shin ina kai littafin zuwa ofishin?

   I don't take the book to the office. bana kai littafin zuwa ofishin.

   Shehu sleeps seven hours every night. Shehu yana yin barcin sa'o'i bakwai a kowani dare.

   Shehu does'nt sleeps seven hours every night. Shehu baya yin barcin sa'o'i bakwai kowane dare.

   Does Shehu sleeps seven hours every night? shin shehu yana yin barcin sa'o'i bakwai kowane dare?

   The president of Nigeria lives in Abuja. Shugaban Nigeria yana rayuwa a Abuja

   Does the President of Nigeria lives in Abuja? shin shugaban Nigeria yana rayuwa a Abuja?

   The President of Nigeria does'nt lives in Abuja. Shugaban Nigeria baya rayuwa a Abuja.

   I play tennis. Ina buga ƙwallon tennis (koda yaushe)

   Do i play tennis? shin ina buga ƙwallon tennis?

   I don't play tennis. bana buga ƙwallon tennis.

   I get up early every day. Ina tashi da wuri kullum.

   Do i get up early every day? shin ina tashi da wuri kullum?

   I don't get up early every night. bana tashi da wuri kullum.


   Usman brushes his teeth twice a day. Usman yana wanke haƙoransa sau biyu a sati.

   Do Usman brushes his teeth twice a week? shin Usman yana wanke haƙoransa sau biyu a sati?

   Usman does'nt brushes his teeth twice a week. Usman baya wanke haƙoransa sau biyu a sati.


   They speak Hausa at school.
   suna magana da harshen Hausa a makaranta.(koda yaushe)

   Do they speak Hausa at school? shin suna magana da harshen Hausa a makaranta?

   They don't speak Hausa at school. Basa yin magana da harshen Hausa a makaranta.

  Kurakurai da gyara

  KuskureGyara Me yasa?
  I working in KanoI work in KanoBa'a anfani da 'ing' a simple present tense
  He work in KanoHe works in KanoDole sai an sanyawa kalmar aikin data biyo bayan third person singular harafin 's' a ƙarshe

 3. Present Continuous Tense:

 4. yana nufin aikin da ake kan yin shi. Akan samad da present continuous tense ta hanyar sanya "ing" a karshen fi'ilin (verb)
  Jimlar da za'a iya anfani da ita zata iya kasancewa positive (jimlar da take tabbatar da magana), za kuma ta iya kasancewa negative (jimlar da take musanta magana) ko kuma question (jimla ta tambaya)

  misali: kalmar "work" tana nufin aiki, to idan kanaso kace kana kan yin aiki, baza kace "i am work" ba, saboda aikin ana kan yin shi ne. Sai dai kace "i am working" ta hanyar sanya "ing"

  Karin misalai

   I am publishing on the internet. ina wallafa bayanai a yanar gizo.

   Am i publishing on the Internet? shin ina wallafa bayanai a yanar gizo?

   I am not publishing on the internet. bana wallafa bayanai a duniyar gizo.

   Shamsuddeen is riding a bicycle. Shamsuddeen yana tuƙa keke.

   Shamsuddeen is not riding a bicycle. Shamsuddeen baya tuƙa keke.

   The boy is running. yaran yana yin gudu.

   I am going to hospital. ina zuwa asibiti.

   We are playing together. muna yin wasa tare.


  Abin lura: A kwai banbanci tsakanin present continuous tense da kuma gerund duk da cewa dai suna kama da juna, misali reading is the way of learning duk da cewa idan kun duba zaku ga aikatau din "verb" sun kare da "ing" ne, amma ba za a lissafa irin wadannan jimlar a cikin "present continuous tense" ba
 5. Past tense:

 6. past tense yana nufin aikin da aka gama yin shi. Idan kalma ta kare da harafin 'e', ana samar da past tense nata ta hanyar sanya 'd' a karshen kalma.
  Misali
  Present TensePast Tense
  carecared
  reposereposed


  Idan kalma ta kare da harafi hade da harafin 'y', ana samar da past tense na wannan kalmar ce ta hanyar cire harafin na 'y', sannan daga bisani a sanya 'ied'.
  Misali:
  Present TensePast Tense
  studystudied
  marrymarried


  Idan kalma ta kare da harafi 'c', ana samar da past tense na wannan kalmar ta hanyar sanya 'ked'
  Misali:
  Present TensePast Tense
  picnicpicnicked


  Ire iren waɗannan kalmomin da za'a iya samar da past tense ɗinsu ta waɗannan hanyoyin sune ake kira 'regular verbs'

  Misalan past tense a cikin jimla

   Last sunday i played my phone loudly and the neighbors complained.
   It rained yesterday.
   Musa wanted to go the museum.

  Amma waɗansu kalmomin baza a iya samad da past tense ɗin su ta hanyar sanya "ed" ko "d" ba. Misali kalmar "write" past tense nata zai zama "wrote"

  Ire iren waɗannan kalmomin sune ake kira 'irregular verbs'

  Misalan past tense na 'irregular verbs' a cikin jimla
   Jibrin was in Zaria yesterday.
   We beat the home team yesterday.
   Umar has become an excellent doctor.
   We bent the branch until it broke.
   My son has broken the window.
   Ibrahim bought a new phone yesterday.

  Tebur ɗinnan na ƙaso ya ƙunshi wasu daga cikin 'irregular verbs' waɗanda ya kamata ace ɗalibin dake koyon turanci ya kiyayesu. Domin su ba kaman 'regular verbs' bane waɗanda suke da sauƙin mayarwa zuwa 'past tense' ta hanyar sanya 'ed' ko kuma 'd' (idan kalmar ta kare da harafin 'e') a'a su sai ka koyesu ɗaya bayan ɗaya. Domin samun cikakken jerin waɗannan verb sai ku duba gurin irregular verb

  Present TensePast TensePast Perfect
  buybought bought
  arisearosearisen
  awakeawokeawakened
  beginbeganbegun
  bindboundbound
  blowblewblown
  breakbrokebroken
  comecamecome
  cutcutcut
  drawdrewdrawn
  drivedrovedriven
  fightfoughtfought
  flyflewflown
  freezefrozefrozen
  givegavegiven
  growgrewgrown
  hidehidhidden
  hurthurthurt
  knowknewknown
  lielaylain
  makemademade
  paypaidpaid
  runranrun
  setsetset
  shutshutshut
  sitsatsat
  stealstolestolen
  springsprangsprung
  taketooktaken
  throwthrewthrown
  bearboreborne
  bendbentbent
  bleedbledbled
  bitebitbitten
  bringbroughtbrought
  choosechosechosen
  creepcreptcrept
  digdugdug
  drinkdrankdrunk
  eatateeaten
  fallfellfallen
  findfoundfound
  forgetforgotforgotten
  getgotgot
  gowentgone
  hearheardheard
  holdheldheld
  keepkeptkept
  laylaidlaid
  loselostlost
  ringrangrung
  putputput
  saysaidsaid
  singsangsung
  sinksanksunk
  speakspokespoken
  swimswamswum
  swearsworesworn
  teartoretorn
  writewrotewritten
  wearworeworn
  winwonwon
  weepweptwept
  windwoundwound
  lightlitlit
  rideroderidden
  riseroserisen

Aika Zuwa

Facebook Twitter Whatsapp

Home

© Copyright 2014 shamsuddeen inc. All right reserved.