Home | About Us | Contact Us | Follow Us On Facebook


Short answer yana nufin gajeruwar amsa.

Cewa, "Yes, i do" ko "No, i don't wajen bayar da amsa yafi nuna girmamawa a maimakon cewa "Yes" ko "No" kawai. Wannan shi yasa akafi yin anfani da short answers a turancin Englishi.

Domin samar da gajeruwar amsa, ana bukatar kayi anfani da kalmar farko ne na tambayar.

Ana bukatar kayi anfani da cikakkiyar kalma wacce ba'a takaita ba domin bayar da affirmative answer (wato amsar dake gasgata magana) misali: "he does"

Amma ana bukatar takaita kalma gurin bayarda negative answer (wato amsar da take musantawa), misali 'he doesn't'

    Misali
TambayaAffirmative AnswerNegative Answer
Do we know him?Yes, we do No, we don't
Can she see me?Yes, she can No, she can't
Have they read the book?Yes, they have No, they haven't
Is he hungryYes, he is No, he isn't

Idan "you" shine "subject" na wannan tambayar, ana bukatar ka canza "you" zuwa "i" ko "we"
    Misali
TambayaAffirmative AnswerNegative Answer
Do you know him?'Yes, i do' ko 'Yes we do''No i don't' ko 'no we don't'

Idan tambayar ta fara da "are you", a wasu lokutan ana bukatar a canza "are" izuwa "am".
    Misali
TambayaAffirmative AnswerNegative Answer
Are you hungry?Yes, i amNo, i'm not
Amma sai dai:Yes, we areNo, we aren't

Aika Zuwa

Facebook Twitter Whatsapp

Home

© Copyright 2014 shamsuddeen inc. All right reserved.