Home | About Us | Contact Us | Follow Us On Facebook


A halin yanzu mun sanya kalmomi kusan dubu ashirin a cikin wannan kamus din. Amma galibi mun sanya ainihin kalmomin ne wadanda ba'a sanya musu kari ba a farko ko karshe domin fidda wata kalmar daga garesu.

Don kuwa ina ganin muddin mutum ya gane asalin kalmar to zai iya gane ma'anar dangoginta.

Akan samad da kalma daga cikin wata kalma ta hanyar amfani da "prefixes" ko kuma "suffixes"

  Prefix:

Wani kari ne da ake sanyawa a farkon kalma domin samad da wata kalmar. Misali "healthy" yana nufin lafiya, amma idan aka sanya "un" a farkon shi, misali "unhealthy", to kalmar ta zama rashin lafiya.

  Suffix:

Wani kari ne da ake sanya wa a karshen kalma domin samad da wata kalmar daman. Misali kalmar "pain" tana nufin "radadi", amma idan aka sanya "less" a karshenta, wato "painless", kalmar ta koma "rashin radadi.

Akwai tarin "prefix" da "suffix" da ake amfani dasu, to amma wannan shafin zai kawo wasu ne kawai daga cikinsu.
  Anti-
ana amfani da shine wajen hana abu ko kore abu, misali "anti-islam" wato makiyin musulinci
  Co-
Ana amfani da shine wajen nuna cewa abubuwa suna tafiya tare, misali "co-worker" abokin aiki
  Ex-
yana nufin abun daya faru a lokutan baya. Misali "ex-student" tsohon dalibi.
  Mid-
yana nufin tsakiya. Misali "mid-night" tsakiyan dare.
  Mis-
Abin da ba'a yishi yanda ya kamataba. Misali "mis-conduct" halayya maras kyau.
  Non-
yana nufin "not" misali "non-smoker" abu mara hayaki
  Over-
yana nufin fiye da kima. Misali "overpopulation" yawan jama'a fiye da kima
  Sub-
yana nufin abun dake cikin wani abu, misali "submenu"
  Dis-
yana nufin "not" misali "dislike" rashin son abu
  In-
yana nufin "not" misali "incorrect" wato kuskure
  Im-
ana amfani da "im" ne kawai idan haruffan "m", "p" ko "b" suka biyo bayan shi. Yana nufin "not" misali, "impossible" abu mara yiwuwa
  il-
ana amfani da "il" ne kawai idan harafin "L" ya biyo bayanshi. Yana nufin "not" misali "illegal" abin da baya kan doka.
  Ir-
ana amfani da shine kawai idan harafin "r" ya biyo bayanshi. Yana nufin "not" misali "irreligious" marasa addini.
  Pre-
yana nufin gabanin. Misali "preview" fara gani tukunna.
  Un-
yana nufin "not" misali "un-islamic" abin da bai shafi musulunci ba
  De-
yana nufin cirewa ko ragewa. Misali "de-activate" wato sanya abu ya dena aiki.
  Dis-
yana nuna "korewa" misali, "dis-agree" rashin yadda
  Bi-
yana nufin abu guda biyu, misali "bicycle"
  Re-
yana nufin sake yin abu, misali "re-establish" sake tsai da abu

  Suffixes

  -ability, -ibility
yana nufin abu mai yiwuwa (makes nouns from adjectives). Misali "responsibility- mai iya daukan alhaki. da aka sama daga kalmar "response"
  _al
ana amfan da shine wajen nuna cewa wani ya aikata wani abu ko wani abu ya faru (makes nouns from verbs). Misali "arribal" isowa da aka fiddo daga kalmar "arrive". Ko "refusal" kin biyayya da aka fiddo daga kalmar "refuse"
  -ation
idan wani yayi wani abu ko idan wani abu zai faru (makes nouns from verbs), misali "confirmation" tabbaci, da aka samo daga kalmar "confirm"
  -ator
yana nuna cewa wani ko wani abu ya aikata wani abu ko yayi sanadiyyar aukuwansa (makes nouns from verbs) misali "creator" da aka samo daga kalmar "create"
  -ity, -ty,
ana amfani dashi ne wajen nuna nau'in halayyar abu (makes nouns from adjectives) misali "stupidity" da aka samo daga kalmar "stupid".
  -ment
Ana amfani dashi ne wajen samar da suna daga cikin fi'ili, misali "development" da aka fiddo daga kalmar "develop", ko "embrassment" da aka fiddo daga kalmar "embrass"
  -ness
ana amfani da shine wajen samar da suna daga cikin siffa (adjective). Misali "happiness" da aka fiddo daga cikin kalmar "happy"
  -able, -ble
akan sa wannan a karken kalma ne don nuna cewa abu mai yuwuwane. Misali "drinkable" abin da zaka iya sha, da aka fiddo daga kalmar "drink"
  -ous
ana amfani da shine wajen kara karfafa kalma. Misali "dangerous" da aka fiddo daga kalmar "danger"

Aika Zuwa

Facebook Twitter Whatsapp

Home

© Copyright 2014 shamsuddeen inc. All right reserved.