Home | About Us | Contact Us | Follow Us On Facebook


    First person
Mutumin da yake magana
    Second person
Mutumin da ake masa magana
    Third person
Mutumin da ake magana a kansa

Abin lura: duk wata kalma ta aiki (verb) data biyo bayan "third person singular" in dai har tana present tense ne, to akan sanya mata "s" ko "es" a karshe (ya danganta ga irin kalmar)

1. Idan kalma ta kare da "s, x, ch, ko "o", to za a sanya mata "es" ne domin maidata "third person singular". Misali.

KalmaThird Person Singular
touchhe touches
washwashes
watchhe watches
finishHe finishes
fixhe fixes
gohe goes
brushhe brushes


2. Idan kalma ta kare da harafin "y" kuma sannan harafi ne kafin "y" din ba wasali ba, to akan samad da "third person singular din shi ta hanyar canza "y" din zuwa "ies"

KalmaThird Person Singular
carryhe carries
studyhe studies
flyhe flies


3. Amma idan akwai wasali kafin "y" akan sanya "s" ne kawai domin maida kalmar third person singular

KalmaThird Person Singular
playhe plays
enjoyhe enjoys
obeyhe obeys
sayhe says


4. Amma wadansu kalmomin sun sha banban

First Person SingularThird Person Singular
i amhe is
i havehe has


5. Kalmomi irin su "shall, will, can, may, must da kuma ought" ba a canza su wajen mai da su third person singular

First Person SingularThird Person Singular
i shallhe shall
i willhe will
i canhe can
i mayhe may
i musthe must

Aika Zuwa

Facebook Twitter Whatsapp

Home

© Copyright 2014 shamsuddeen inc. All right reserved.