Home | About Us | Contact Us | Follow Us On Facebook


Idan kuka duba ilahirin kalmomin dake cikin kamusun mu, zaku ga kusun kowace kalma tana dauke da haruffan furuci na IPA (wato international phonetic alphabets) wasu haruffa na kasashen duniya da ake anfani dasu gurin rubuta yadda ake furta kalmomin kowane yare na duniyan nan. Sanya wadannan haruffan furucin da muka yi yana da muhimmanci domin mutane su fahimci yadda ake furta kowace kalma ta turanci. Galibi yanda ake rubuta kalmomin turanci ba haka ake furta su ba. Don haka yana da muhimmanci a duk lokacin da mutum yake shakka akan yadda ake furta kalma to ya duba a kamus.

Wannan karamin shafin mun tsara shine musamman domin fahimtar da mutane IPA na kalmomin turancin Birtaniya.

 1. Haruffa (consonants)


 2. A turanci muna da haruffa guda goma sha biyar kaman haka. b, d, f, h, k, l, m, n, p, r, s, t, v, w, and z. Ganin cewa da akwai banbance banbance tsakanin yadda ake furta wasu haruffa tsakanin turanci da kuma Hausa, zamu yi anfani da kalmomin turanci ne domin misalta yadda ake furta haruffan turanci.

  IPA

   

  Misalai

  ɡ

  as in

  get  

   

  chip 

  ʤ

   

  jar 

  x

   

  loch

  ŋ

   

  ring

  θ

   

  thin

  ð

   

  this

  ʃ

   

  she

  ʒ

   

  decision

  j

   

  yes

 3. Wasulla (vowels)
 4. IPA

   

  Misalai

  Short vowels

   

   

  a

  as in

  cat

  ɛ

   

  bed

  ə

   

  ago

  ɪ

   

  sit

  i

   

  cosy

  ɒ

   

  hot

  ʌ

   

  run

  ʊ

   

  put

  Long vowels

   

   

  ɑː

   

  arm

  ɛː

   

  hair

  əː

   

  her

   

  see

  ɔː

   

  saw

   

  too

  Diphthongs

   

   

  ʌɪ

   

  my

   

  how

   

  day

  əʊ

   

  no

  ɪə

   

  near

  ɔɪ

   

  boy

  ʊə

   

  poor

  Triphthongs

   

   

  ʌɪə

   

  fire

  aʊə

   

  sour

Yana da Muhimmanci mutum ya fahimci wadannan IPA, Amma idan kana ganin hakan duk jidali ne, to ta kwana gidan sauki, tunda dai a yanzu akwai saututtuka na yanda ake furta kowace kalma na turanci wadanda za'a iya saukarwa akan na'urorin zamani. Yaku iya yin anfani da wannan shafin www.fromtexttospeech.com domin saukar da duk wata kalma koma jimla ta turanci da ake son koyan furucin ta.

Amma yana da muhimmanci a duk lokacin da mutum zai saukar da furucin kalma ya sani cewa turancin Birtaniya (British English) shine turancin da muke anfani dashi a Naijeriya ba Turancin Amurka (American English) ba. Da yawa daga cikin masu kera manhajojin Turancin Ingilishi Amurkawa ne da suke anfani da turancin Amurka, kuma sauda yawa da akwai banbance banbancen yanda ake furta kalmomi tsakanin turancin Amurka dana Birtaniya.

Aika Zuwa

Facebook Twitter Whatsapp

Home

© Copyright 2014 shamsuddeen inc. All right reserved.