Home | About Us | Contact Us | Follow Us On Facebook


Modal verbs a turancin ingilishi sune kamar haka: can, could, must, will, would, should, shall, may, might. Sannan kuma wadannan kalmomin suna aiki kusan kamar modal verbs

ought to, have to, got to

Galibi ana rubuta wadannan irin kalmomi a takaice ne, don haka zamu rubuta 'can't' a maimakon 'cannot', 'mustn't' a maimakon 'must not' 'wouldn't' a maimakon 'would not'

Zaku iya yin anfani da modal verbs domin bada taimako, neman shawara ko bayar da shawara, neman izini ko kuma domin bayar da izini.

Misalan modal verbs a cikin Jimla

  1. Ana anfani da modal verbs (can, will, could, would) domin neman alfarma.
Misali:

EnglishFassarar Hausa
Can you help me, please?Ko zaka iya taimaka mini, don Allah?
Will you close the door?Ko zaka iya kulle tagar?
Could you tell me the time, please?Ko zaka iya gaya mini lokaci, Don Allah?
Abun lura: 'could' da kuma 'would' sunfi karɓuwa kuma sunfi nuna girmamawa
  2. Ana anfani da modal verbs (can, could, may) domin neman izini ko bayar da izini
EnglishFassarar Hausa
You can borrow my carZaka iya arar motata
Can i have some more soup?Ko zan iya samun karin miya?
Could i speak to the manager, please?Ko zan iya samun daman yin magana da manajan don Allah?
May i go to the cinema, please? Ko zan iya zuwa cinema?
Abun lura: 'could' yafi nuna girmamawa fiye da 'can'. sannan kuma anfi yin anfani da 'may' a karɓaɓɓen turancin ingilishi
  3. Ana anfani da modal verbs (can, may, shall, will) domin bayar da taimako
EnglishFassarar Hausa
Can i give you a hand?Ko zan iya miko maka hannu?
May i help you?Ko zan iya taimaka maka?
Shall i carry your bag?Ko zan iya daukan jakarka?
I'll show you the wayZan nuna maka gurin
  4. Ana anfani da modal verbs (should, ought to, shall and must) domin bayar da shawara ko kuma domin neman shawara.
EnglishFassarar Hausa
You should take more exerciseYana da kyau ka samu motsa jiki sosai
You ought to go to the dentist'sYa kamata kaje gurin likitan hakora
Shall we try again?Ya kamata ace mun sake kokartawa kuma?
You must try this cake- it's delicious!dole ne ka jaraba wannan gurasar domin tana da dandano mai daɗi
  5. Za kuma ku iya yin anfani da modal verb (must, can't will) domin cewa dole abu Ya faru
EnglishFassarar Hausa
He must be here already- there's his car.dole ne ya zamana ya riga yazo, domin akwai motarsa a gurin
She's late. She must have missed the bus.ta makara, don haka dole ya zamana ta kurkure motar safar
You can't have finished already.Ba zai yiwu ace ka kammala tuntuni ba!
we won't be beaten.baza a dakemu ba
I shan't forget you.bazan taba mantawa da kai ba.
  6. Ana anfani da modal verbs (should, ought to) domin nuna abun da ake tsammanin zai faru
EnglishFassarar Hausa
it ought to be finished by tonightYa dace a gama shi daga nan zuwa dare
it's only a headache- i should feel better in the morningciwon kai ne kawai nake fama dashi, ina sa ran zan samu sauki da safe.
  7. Ana anfani da modal verbs (may, could, might) domin nuna abu mai yiwuwa
EnglishFassarar Hausa
I think i may be late home tonightIna ganin zan iya makara zuwa gida da dare
it could be in the cubboard- i'm not sure.Zai iya yiwuwa abun yana cikin cubboard, amma ban tabbatar ba
i might have left it on the bus, i can't remember.Zai iya yiwuwa na barsa a cikin mota, amma bazan iya tunawa ba
  Wasu daga cikin kura kuren da ya kamata ku lura dasu
Ba zai yiwu ace kalmar "to" ta biyo bayan modal verbs ba.Ba'a sanya wa modal verbs 's' domin maidashi third person singular

Aika Zuwa

Facebook Twitter Whatsapp

Home

© Copyright 2014 shamsuddeen inc. All right reserved.