Koyon Turanci Da Hausa


Home | About Us | Contact Us | Follow Us On Facebook


ME yiwuwa mafi yawancin mutanen da suke shigowa wannan shafin sun ɗauki shekaru suna ƙoƙarin koyan turanci, amma kuma duk da haka basu samu nasara ba. Don kuwa an daɗe ana ta aiko mini da wannan tambayar. Shin wata hanya ce mutum zai bi domin koyan turanci.

To na daɗe dai ina yin gum da baki na ba tare da amsa irin waɗannan tambayoyin ba, saboda ina buƙatan nayi nazari mai tsawo tukunna.

Shin turanci yare ne mai sauƙin koyo? Amsar itace, 'ya danganta ga yaren da mutum ya fara koyo a matsayin harshen sa na gado lokacin yana ƙarami'. Misali ganin cewa yawancin kalmomin turancin English sun samo asali ne daga cikin turancin French; English zai iya zamantowa mai matuƙan sauƙi ga mutumin da Faransanci shine harshen sa na gado. Kaman dai a Naijeriya ne, da akwai wani irin gurɓataccen Turanci da ake anfani dashi a kudanci da tsakiyar ƙasar da ake kira 'broken English' ko pidgin English, ganin cewa wannan yaren ya ginu ne da salan harsunan Naijeria, irin wannan turancin yana da matuƙan sauƙin koyo ga mutanen wannan ƙasar.

To amma ba wai na kashe maka jiki bane, Turanci na Ainihi yana da matuƙan wahala da kuma ɗaukan tsawan lokaci kafin samun ƙwarewa a kanshi ga mutumin daya kasance ɗaya daga cikin harsunan Naijeriya shine yaran sa na gado.

A yanayin yanda tinanin mutane yake, mutane sun kasance suna kwaikwayon salon harshen su na gado ne a yinƙurin koyon anfani da kalmomi domin haɗa jimla a wata sabuwar yare da suke shirin koyo. Hakan ne yasa koyon wani sabon yare yake da matuƙan wahala saboda galibi da akwai banbance banbance masu yawa akan yanda ake haɗa jimla tsakanin wannan yaren da wancan. Shi yasa zai ɗauki mutum tsawan lokaci kafin ya sauya wannan tunanin. Sanin ma'anan kalma kawai bazai sa mutum ya iya yin magana da yare ba, face yasan yanda ake anfani da kalmomin a cikin jimla. Wannan ne yasa muke kawo misalan kowace kalma a cikin ƙamusun mu domin mutane su san yanda ake anfani da kalmomin.

Kusan ma zan iya cewa ba abu ne mai yiwuwa ba mutum ya iya ƙwarewa a turanci ta hanyar karatu kawai. Don haka ban baka shawarar ka ɓata lokaci wai lalle sai ka koya turanci mai tsauri ba. Tun da dai turanci ana koyan shi ne kawai domin sadarwa, to da zaran ka koyi turanci mai sauƙi ma ya isa ka iya yin mu'amala da masu magana da turanci.

Kasancewar Turancin English shine lingua franca na duk duniya (wato yaren da mutanen da basa jin yaren juna suke anfani dashi domin sadarwa tsakanin su); hakan yasa a kullum sai ƙaruwar masu sha'awan koyan turanci ake ta samu daga sassa dabam daban na duniya. Kuma galibi sukan koyi simple English ne, wannan ne yasa turanci mai sauƙi (simple English) shi ne turanci mafi karɓuwa a duniya a halin yanzu. Domin shine turancin da koda mutum bai ƙware a turanci sosai ba zai fahimta

Hanyoyin da mutum zai bi domin koyon turanci sune kamar haka:

Hanya mafi sauƙi ta koyon turanci koma ta koyan kowani yare itace ta hanyar yin mu'amala da mutanen da suke yin magana da wannan yaren. To amma duk da haka masana sun dage cewa lalle za'a iya koyan yare ta hanyar bin manhajojin karatu. Hanyoyin kuwa sune kamar haka:

Hanya ta farko

Koyon rubutawa tare da karanta rubutun turanci shine abu na farko da mutum zai fara dashi. A bayan da mutum ya ƙware gurin karantawa tare da rubuta turanci, (misali bayan da mutum ya kammala makarantar firamare) zai iya ɗaukan mutum shekaru biyar wasu ma har zuwa shekaru bakwai kafin mutum ya zama ƙwararre gurin rubutawa tare da yin magana da harshen turanci.

Koda yake ya danganta ga irin horan da mutum ya samu da kuma saurin fahimtar da mutum yake dashi. Don kuwa wasu yaran ma tun suna aji huɗu na makarantun firamare suke ƙwarewa gurin rubutawa tare da karanta rubutun turanci. Don ni kaina na ƙware gurin rubutawa tare da karanta rubutun Hausa lokacin ina aji uku a firamare, sannan kuma na ƙware gurin rubutawa da karanta turanci lokacin ina aji huɗu a firamare. Domin sanin hanyar dana bi domin koyon karatun hausa da turanci ka duba gurin shin zai yiwu mutum ya koyi karatu ba tare da malami ba?

Koyon karatu tare da rubuta turanci abu ne mai matuƙan sauƙi ga hausawa waɗanda suka fara koyon karatun Hausa. Don kuwa ina ganin a cikin watanni shida kawai mutum zai iya ƙwarewa gurin rubutawa tare da karanta turancin English.

Hanya ta biyu

a bayan da mutum ya ƙware gurin karantawa tare da rubuta Turanci, abu na gaba kuma shine vocabulary, wato sanin ma'anan kalmomin Turanci. A ɗabi'ance, mutane sun kasance suna haddace kalma ce ta hanyar fassarata kai tsaye da yaren da suka fara koyo, wato harshen su na gado. Hakan yasa bahaushe zai yi sauƙin haddace kalmomin Turanci saboda da yawa daga cikin kalmomin Turanci za'a iya fassara su kai tsaye zuwa Hausa.To ta yaya mutum zai fara?

A lalace ina ganin da akwai kalmomi dubu goma sha takwas a cikin oxford dictionary, Hakan yana nufin dole sai mutum ya san dukkan waɗannan kalmomin kafin ya zama ƙwararre a Turanci? A'a, ba dole bane, ana buƙatan mutum yasan kalmomin da aka fi yin anfani dasu a Turanci ne kawai. Idan mutum ya mallaki dictionary na oxford ko longman, zai ga suna ware wasu kalmomi guda dubu uku, waɗanda ƙwararru a fannin turanci suka yi ittifaƙin cewa sune kalmomin da aka fi yin anfani dasu a turanci. Don haka mutum zai fi bada muhimmanci a gare su gurin gina vocabulary nasa. Mun tsara waɗannan kalmomi a matsayin manhaja ta wayar tafi da gidan ka

Download Vocabulary wordlist for Android

Download Vocabulary wordlist for windows mobile

idan kuma kana anfani da wata wayar ce to zaku iya karanta waɗannan kalmomin tare da ma'anoninsu a nan.

Hanya ta uku

A bayan da mutum ya haddace kalmomi kuma, abubuwa biyu na gaba kuma waɗanda dole su tafi lokaci guda, sune grammar da kuma comprehension.

grammar yana nufin 'nahawu' (wato ƙa'idojin da ake bi gurin yin magana da turanci). Sannan kuma comprehension yana nufin 'fahimtar yanda ake anfani da kalma a cikin jimla'.

Koyon grammar abu ne mai matuƙan sauƙi, idan mutum ya mayar da hankali a cikin wata ɗaya zai iya ƙwarewa a grammar. Abun da nake ganin kawai zai ba mutane wahala shine 'Tenses', ƙwarewa a Tenses mai yiwuwa zai ba Hausawa wahala, saboda a Hausa bamu da yawancin waɗannan Tenses

Hanya ta huɗu

Abu na gaba kuma shine comprehension, wato sanin yanda ake anfani da kalmomi a cikin jimla. comprehension abu ne mai matuƙan wahala, kuma zai iya ɗaukan mutun shekaru uku zuwa biyar kafin yasan yanda ake anfani da kowace kalmar Turanci a cikin jimla. Kalmomin turanci suna ɗaukan ma'anoni mabanbanta kuma ana anfani dasu a sigogi dabam dabam. Misali kalmar provide tana nufin 'samar da' past tense na wannan kalmar shine provided, wato yana nufin abun da aka riga aka samar. To amma kuma duk da haka kuma kalmar provided a wasu lokutan kuma tana nufin 'Matuƙan dai'. Duba misalan wannan kalmar a cikin jimla.

  1. A project designed to provide young people with work. wani shiri da aka tsara domin ya samar da aiki ga matasa.
  2. The project provided nothing to young people. Shirin bai samar da komai ba ga matasa.
  3. You can buy anything here, provided you have sufficient fund. zaka iya siyan komai anan, matuƙan dai kana da wadataccen kuɗi.

Misali na biyu

Kalmar behind duk da cewa tana nufin 'a baya' ne, to amma fassara wannan kalmar zuwa Hausa abu ne da ba zai yiwu ba, domin takan canza ma'ana a wasu lokutan, ya danganta ga irin jimlar da aka sanya ta a ciki.

Misali:

  1. A baya: who's this standing behind you? waye wannan yake tsaye a bayan ka?
  2. Zamantowa koma baya: He's behind the rest of the class in reading. shi ne koma baya a ajin gurin yin karatu.
  3. Goyon baya: She knew that, whatever she decided her family was right behind her. ta san cewa duk shawarar data yanke, iyalanta zasu goya mata baya.
  4. Zamantowa mai alhakin faruwan wani abu: He was the man behind the plan to build a new hospital. Shine mutumin da yake da alhakin shirin gina sabon asibiti.
  5. A gurin: I was told to stay behind after school. an gaya mini dana tsaya a gurin bayan tashi makaranta.
  6. Abun dake tattare da abu: What is behind these expensive cars? Me ke tattare da waɗannan motocin masu tsada?

Waɗannan kalmomin biyu somin taɓi ne kawai daga cikin kalmomi masu rikitarwa da za kuyi ta cin karo dasu a cikin turanci, kuma dole mutum yasan yanda ake anfani da kowace kalma kafin ya ɗauki kansa a matsayin ƙwararren masanin Turanci. Wannan ne yasa mutane da yawa zasu daɗe suna koyan turanci, amma duk da haka idan suka ɗauko wani littafin turanci suna karantawa, gabaki ɗaya sai su raina turancin su. Domin na lura mafi yawancin mutane, musamman a Nigeria suna da ɗabi'an son yin magana da turanci mai wahala, domin kawai su birge mutane a riƙa yi masu kallon masu ilimi, to amma kuma idan kaje ka dawo kuma zaka ga suna mayar da kansu tamkar wasu sakarkaru ne. Domin kuwa zasu yi magana amma cikin mutane ɗari da suke sauraren su bai wuce a samu mutane goma da suke fahimtar abun da suke cewa ba, ashe kuwa burgewa bata yi rana ba.

Mafi yawanci nan Nigeria bama ɓata lokacin mu gurin koyon turanci mai tsauri, tun da dai turanci ana koyan shi ne domin sadarwa tsakanin mutane, don haka da zaran mutum ya ɗan iya turancin daya isa ya iya yin mu'amala tsakanin mutane kawai shi kenan.

Yanda ake anfani da kalmomi domin fitar da jimla a turanci galibi ya saba da yanda ake anfani dasu a harsunan Naijeriya.

Wace hanya ce tafi dacewa mutum ya bi domin koyon comprehension?

Hanyar da tafi dacewa abi domin koyan comprehension ita ce karanta littattafan da aka rubutasu da ingantaccen turanci, wannan ya haɗa da littattafan adabi (Nobel), jaridu ko mujallu ko kuma shafukan yanar gizo. Amma dai nafi bada shawaran ayi anfani da Nobel (littattafan ƙagaggun labarai), kuma dole ne ya kasance da akwai dictionary a kusa da kai saboda yawanci ire iren waɗannan littattafan suna yin anfani da kalmomi masu tsauri. Kuma sannan daga lokaci zuwa lokaci yana da muhimmanci mutum ya riƙa gwada ƙwarewarsa ta hanyar rubuta wani labari da turanci, domin ganin irin ci gaban daka samu a harshen Turancin. Ko kuma hanya mafi sauƙi ma tun da da akwai social network, yin musayar saƙonni da mutanen da suke anfani da ingantaccen turanci zai matuƙan taimakawa mutum ya sabawa ƙwaƙwalwarsa ta fahimci yanda ake anfani da kalma.

Abu na biyar

Abu na biyar kuma shine Oral English. Oral English yana nufin 'Turancin baki' wato yanda ake furicin kalmomi. Oral English yana daga cikin abu mafi wahala da mutanen Naijeria suke fama dashi. Ba wai na katse maka hanzari bane, amma dai matuƙan dai a Naijeriya ka girma, to kuwa zai yi wahala ka iya yin magana da turanci ba tare da ansan cewa kai ba bature bane. Misali kuwa da zan baka shine idan wani ƙabila yazo nan arewa daga kudu, kuma yazo ne baya jin Hausa, sai daga baya yazo ya koyi Hausan sakamakon cuɗanya da Hausawa, zaka ga duk da cewa ya ƙware a Hausar, amma da zaran yayi magana sai kasan cewa ba bahaushe bane. To amma kuma sai kaga yaran shi daya haifa a ƙasar Hausa kuma ya girma a cikin Hausawa, shi kuma da zaran yayi magana in ban da kamanni zaka ɗauka bahaushe ne.

To amma duk da haka mutumin Naijeriya zai iya yin magana da turanci a cikin turawa kuma su fahimci abin da yake cewa. Duk da cewa bamu sanya darasin Oral English a cikin wannan shafin namu ba tukunna, to amma zaka iya dubawa a wasu guraren.

Abu mafi muhimmanci a darasin Oral English shine sanin yanda ake furta kalmomi. Wannan ko abu ne mai sauƙi, domin kuwa da zaran kana kokwanto akan yanda ake furta kalma, to abun da zaka yi kawai shine ka duba dictionary. Mafi yawancin dictionary suna rubuta yanda ake furta kowace kalma. ko kuma abu mafi sauƙi yanzu da akwai manhajojin wayoyin salula da suke ɗauke da sautin yanda ake furta kalmomin turanci da zaka iya saurara. Amma yana da muhimmanci ka tabbatar da cewa British pronouncition ne ba American pronouncition ba. Don kuwa da akwai banbance banbance masu yawa tsakanin yanda ake furta kalmomi a Turancin Birtaniya da kuma Turancin Amurka. Turancin Birtaniya shine turancin da muke anfani dashi a Naijeriya ba turancin Amurka ba.

Mafi yawancin kalmomin Turanci yanda ake rubuta su ya banbanta da yanda ake furta su. Misali kalmar knowledge, duk da cewa an sanya haruffan 'k' da 'd' a cikin kalmar, to amma ba'a ambaton waɗannan kalmomin gurin furta wannan kalmar, ana furta wannan kalmar ce da nolej

Haka ma kalmar psychology duk da cewa an sanya harafin 'p' a farkon kalmar, amma duk da haka ba'a ambaton wannan harafin gurin furta kalmar. Kuma duk da cewa a bisa ƙa'ida cho ana furta shi ne a matsayin 'co', amma duk da haka a wannan kalmar ana furta shi ne a matsayin 'ko', don haka ana furta wannan kalmar ce da saikoloji.

Wannan kaɗan kenan daga cikin kalmomi masu rikitarwa da dole sai mutum ya iya furta kowace kalma ta turanci kafin ya ɗauki kansa a matsayin ƙwararren masanin Turanci.

Aika Zuwa

Facebook Twitter Whatsapp

Home

© Copyright 2014 shamsuddeen inc. All right reserved.