Home | About Us | Contact Us | Follow Us On Facebook


Future tense yana nufin aikin da zai faru a nan gaba (lokaci mai zuwa)

Za'a iya yin anfani da "will", "going to", ko "shall" domin samar da future tense

    Will

TuranciFassara
I think he will phone me laterIna tunanin zai kira lambata anjima
The rain will stop soon ruwan zai dauke bada jimawaba
There is a noise outside, i will just go and check Akwai hayaniya a waje, bari inje in duba
You will report to me at eight o'clock tomorrowZaka kawo min rahoto da karfe takwas gobe
They will invite Dr. Zakir Naik to speak at the scientific conference Zasu gayyato Dr. Zakir Naik domin yayi magana a zauran taron kimiyyar
Give me your mobile phone or i will slit your throat with this knifebani wayar salularka ko kuma in tsaga wuyarka da wannan wukar
I will try not to be late againZan tabbatar cewa ban sake makara ba

    going to

Zaka iya yin anfani da "going to" domin samar da future tense

TuranciFassara
We are going to visit the zoo on SundayZamu kai ziyara gidan dabbobin dajin ranar lahadi
he thinks his son's team is going to win the match Yana zaton cewa kungiyar 'yan wasan da yaransa ke buga wasa a cikin ta zasu yi nasara a gasar da za'a buga
My son is going to be ten years old next month Yaro na zai cika shekaru goma a wata mai zuwa
we are going to leave as soon as Musa arrivesZamu bar gurin da zaran Musa ya iso
We are going to the market when it stops rainingzamu tafi kasuwa idan ruwa ya tsaya
i am going to be at the meeting tomorrow zan kasance a cikin taron gobe
we are going to visit Sama'ila in the hospital tomorrowzamu ziyarci Sama'ila a asibiti gobe
we are going to visit them again early next monthZamu sake ziyartarsu a farkon wata mai zuwa

    Za a iya anfani da "ing" domin samar da future tense

TuranciFassara
Shehu is leaving the company next weekShehu zai bar Masana'antar sati mai zuwa
We are visiting the Maiduguri of Borno state in three weeks Zamu ziyarci Maidugurin Jihar Borno cikin sati uku
My father is writing another book next month Mahaifina zai rubuta wani littafi wata mai zuwa
He is attending a seminar tomorrowZai halarci taron kara wa juna sani gobe

    Shall

Ana yin anfani da "Shall" ne ga first person kawai. Misali:

TuranciFassara
I shall be away tomorrowZan yi nisan kiwo gobe
we shall be away tomorrowZamuyi nisan kiyo gobe

Aika Zuwa

Facebook Twitter Whatsapp

Home

© Copyright 2014 shamsuddeen inc. All right reserved.