Home | About Us | Contact Us | Follow Us On Facebook


Capital letters suna nufin manyan haruffa, misali:
CAPITAL LETTERS small letters

1. Ana anfani da capital letters a duk harafin farkon sunan mutum, misali Ahmad, Yunus, Auwal, Maryam

2. Ana anfani da capital letters a duk harafin farkon sunan wani gari. Misali: Nigeria, Kaduna, Zaria

3. Ana anfani da capital letters a duk harafin farkon sunan littafi mai tsarki. Misali: Al-qur'an, Bible

4. Ana anfani da capital letters domin banbance sunan Ubangiji mahalicci da kuma abin da wasu suke bautawa wanda ba Allah ba. Misali "God" yana nufin Ubangiji mahalicci, yayin da "god" yake nufin abin da wasu ke bautawa wanda ba Allah ba. "Lord" Yana nufin Ubangiji mahalicci, ayayin da "lord" za a iya anfani dashi a mutane

5. Ana anfani da capital letters a duk farkon wata Jimla.

6. Ana anfani da capital letters a duk farkon sunan ranaku ko watanni. Misali: Monday, Tuesday, Friday, November, December.

7. Ana anfani da capital letters a duk farkon sunan Addini. Misali: Islam, Judaism, Christianity.

Aika Zuwa

Facebook Twitter Whatsapp

Home

© Copyright 2014 shamsuddeen inc. All right reserved.