Home | About Us | Contact Us | Follow Us On Facebook


A turanci muna da haruffa guda ishirin da shida ne kamar haka A kowani kamus akan sanya kalmomi ne a jere bisa irin harafin da kowace kalma ta fara dashi. Misali kalmar 'bell' ta zone kafin kalmar 'find' saboda harafin farko na kalmar 'bell' wato 'b' yazo ne kafin harafin farko na kalmar 'find' wato 'f' a jerin haruffa.

1. Za'a iya jera kalmomi a bisa irin haruffan da kowacce kalma ta fara da ita. Misali: adult, bold, hard, poor, small, up, zebra.

2. Za a iya jera kalmomi ta la'akari da harafi na biyu da kalmar take dashi idan harafi na farko da kowace kalma take da shi iri guda ne. Misali: pass, pen, place, pot, press, purse.

3. Za'a iya jera kalmomi ta hanyar la'akari da haruffa na uku da kowacce kalma take dashi idan haruffa biyu na farko da kalmomin suke dashi duk iri guda ne. Misali: field, fight, fill, find, fish, fit.

4. Haka ma za'a iya jera kalma ta la'akari da harafi na hudu da dai sauransu.

Aika Zuwa

Facebook Twitter Whatsapp

Home

© Copyright 2014 shamsuddeen inc. All right reserved.