1. Shin kalmomi nawane a cikin wannan ƙamus ɗin yansu?

Babu wata kalmar turanci ko kalmar hausar da bamu sanya a cikin wannan ƙamus ɗin ba in banda wasu 'yan kaɗan kodai saboda mun kasa fassara su ko kuma saboda rashin muhimmancin su da muke gani. Bamu tsaya a sanya kalmomi kawai ba, kusan kowace kalma mukan kawo misalanta a cikin jimla domin mutane susan yanda ake anfani da kalmar.

2. To amma me yasa sauda yawa idan na bincika ban samun wasu kalmomi a ciki?

Idan aka bincika ba tare da samun sakamako ba to adai duba da kyau ko anyi kuskuren rubuta kalmar da ake bincike, in kuma har kalmar dai dai ce, to

Yana da kyau a lura da cewa:

  1. Bamu sanya haruffa masu lanƙwasa, saboda script da muke anfani dashi a halin yanzu yana da matsalar nuna ire iren waɗannan haruffan. A maimakon haka mukan sanya wannan alamar ' a matsayin lanƙwasa. Misali, k', b', d', don haka domin bincika kalmomi masu lanƙwasa ana buƙatar a sanya wannan alamar ' a gaban harafin. Misali, k'ashi, b'oye, d'umi
  2. Bamu sanya kalmomin 'plural' waɗanda ake samad da su ta hanyar sanya 's' ko 'es' a ƙarshen kalma
  3. Galibi bamu sanya kalmomi masu ɗauke da 'past participle' (waɗanda ake sanya musu 'ed' ko 'd' a ƙarshensu)
  4. galibi bama sanya kalmomi masu ɗauke da 'present perticiple' wato kalmomin da ake samar dasu ta hanyar sanya haruffan 'ing' a ƙarshen kalma. Misali kalmar 'going' wacce aka samad da ita daga cikin kalmar 'go'
  5. Bamu sanya 'comparative' da kuma 'superlatives' na 'adjectives' (misali 'low' {ƙaranci}, lower {matsakaici} sai kuma 'lowest' (mafi ƙaranci) mukan sanya 'Adjectives' ɗin ne kawai, wato 'low'
  6. akwai waɗansu kalmomi waɗanda suke ɗauke da 'prefix' ko kuma 'suffix' waɗanda muka tsallake bamu sanyasu a cikin wannan ƙamus ɗin ba
  7. Don haka yana da muhimmanci ku duba waɗannan shafukan na ƙasa domin sanin yanda kalmomi ke canzawa, don kuwa ina ganin muddin mutum ya gane asalin kalma to zai iya gane ma'anan dangoginta
Singular And Plural

Prefix And Suffix

Tenses

Adjectives

Muddin mutum ya gane asalin kalma to zai iya gane ma'anar dangogin ta, misali kalmar 'appreciate' ana fidda kalmomi har bakwai daga cikinta kamar haka: 'appreciates, appreciator, appreciatory, appreciable, appreciation, appreciative, appreciating,' sannan kuma bayan an fidda waɗannan kalmomin bakwai, suma haka za a iya fidda wasu kalmomin daga cikinsu kamar haka: 'appreciatively, appreciativeness, appreciable, appreciably, appreciatingly' to idan kun duba zaku ga kalma ɗayace 'appreciate' amma ta zama goma sha biyu. idan mutum baida masaniya akan darasin 'suffix' zai iya tunanin cewa ko waɗannan wasu kalmomine mabanbanta, amma a zahiri waɗannan kalmomin goma sha biyu duk suna ɗaukan kusan ma'ana guda ne. Kaman dai a hausa ne kalmar 'aiki' akan fidda kalmomi har goma sha huɗu daga cikinta kamar haka: 'ayyuka, aika aika, ma'aiki, ma'aikiya, ma'aikaci, ma'aikaciya, ma'aikata, (gurin aiki), ma'aikata (masu aiki), ma'aikatu, ma'aika, aikace, aikatau, aikatu, aikatuwa'. To kaman hakane misalin kalmomin turanci masu ɗauke da 'suffix' yake, muddin kuka gane haruffan da ake anfani dasu gurin canza kalma to bakwa buƙatan neman bincika ma'anan kalmomi masu ɗauke da 'suffix'. Domin koyon wannan darasin sai ku duba gurin 'prefix and suffix'

3. Me yasa wasu lokutan idan na bincika kalma na ke samun fassarar da ta banbanta da wacce na samu a wasu ƙamus ɗin?

Muna yin anfani da Longman Dictionary da kuma oxford dictionary ne wajen zaƙulo kalmomin da daga bisani muke fassara su zuwa hausa. A zahiri a wasu lokutan akan samu saɓanin fassara tsakanin wasu "dictionaries" ɗin. Kuma sannan waɗansu kalmomin na ɗaukan ma'anoni daban dabam. Domin neman ƙarin bayani duba shafin homonyms

4. Me yasa nake ganin kalmomi da yawa kuna yi musu fassara iri guda?

e, turanci yana da wannan, domin neman ƙarin bayani duba shafin synonyms

5. Me kuke nufi da "idan akai anfani da kalmar a lokacin da ya wuce"?

muna nufin kalmar ko dai "past tense" ce ko "past perfect tense" don neman ƙarin bayani duba shafin tenses

6. Na samu wasu kalmomin da kuka rubutasu ba yanda ya kamata ba, ko kuka fassara su da fassarar da ba shine ya dace da su ba.

muna maraba da shawarwari ko kuma gyara idan an samu kuskure a cikin wannan ƙamus ɗin ko ma dai sashin koyon turanci na wannan website. Zaku iya tuntubanmu ta nan

7. Me yasa wannan shafin baya aiki yadda ya kamata akan wayar salula?

Mun gwada wannan shafin kuma yana aiki yadda ya kamata akan wayar Nokia mai ɗauke da manhajar Opera Mini browser, Mafi karanci version 4.2, don haka bamu da alhaki idan ka ziyarci wannan shafin ta hanyar anfani da wata wayar daban. Kuma sannan koda za ka ziyarci wannan shafin ta hanyar anfani da opera mini, to indai kanaso yai aiki yadda ya kamata to dole kai "enable" desktop view ko kuma "disable" mobile view. Amma duk da haka idan akwai wata matsala da kuke samu wajen anfani da shafin akan wayar salula to kuyi saurin sanar damu domin mu duba