meaning of carry in Hausa | Hausa Dictionary | English Hausa Dictionary
kamus
Hausa Dictionary
Our App | Koyon Turanci |Quran Search


English Hausa Dictionary/Kamus

English To Hausa Hausa To English© Copyright 2014-2021 Shamsuddeen Inc. All right reserved

Definition of carry in Hausa

carry

verb /ˈkæri/
1. Ɗauka
2. Riƙe
3. Jigila
4. Ɗauke da
5. Ɗaukan ciki
6. Ci gaba

Example of carry in a sentence

Carry
  
 1. Ɗauka
 2. He carried a bag. ya ɗauki jaka.

  I carried the heavy bag to office. na ɗauki jakar mai nauyi zuwa ofis.

  A small child cannot carry this bag because the bag is heavy. ƙaramin yaro bazai iya ɗaukan wannan jakar ba saboda tana da nauyi.

  Someone entered our house and carried off our belongings. wani ya shiga gidan mu ya kwashe mana kayayyakin mu.

 3. Jigila
 4. A bus carrying bank staff was intercepted by kidnappers. masu satan mutane sun tsare wata mota mai ɗauke da ma'aikatan banki.

  A wire from the city carry electricity to all rural areas. waya daga cikin birnin tana kai wutar lantarki dukkanin yankunan karkaran.

  Bello carry all his children to school on his bike. Bello yana kai dukkan yaran shi makaranta akan keke.

  Most women in Nigeria carry their infants on back. yawancin mata a Nigeria suna ɗaukan jariran sune a baya.

  Nobody carried the abandoned bag. babu wanda ya ɗauki jakar da aka jefar.

  Synonyms (kalmomi masu alaƙa)
  cart, transport

 5. Riƙe
 6. She carried her baby in her arms. ta riƙe jaririnta a hannunta.

  Police in Nigeria carry sticks instead of guns occasionally. a wasu lokutan 'Yan sanda a Nigeria suna riƙe sanda ne a maimakon bindiga.

  A child who was abused at young age usually carry the memory of the incident into adulthood. yaran da aka ci zarafin shi lokacin yana ƙarami zai riƙa tunawa da wannan abun har ya girma.

  She's a sex worker who always carries condom in her purse. ita karuwa ce wacce a koda yaushe take yawo da kwaroron roba a cikin jakarta.

  Muggers have once snatched my purse since then i stop carry money in a purse. 'yan fashi sun taɓa fisge jakar hannu ta kuma tun daga wannan lokacin ne na daina yawo da kuɗaɗe a cikin jaka.

  It is criminal offense to carry weapons in Nigeria. ɗaukan makamai laifi ne a Nigeria.

 7. Ɗauke da
 8. Most Chinese products carry the phrases 'made in China'. yawancin kayayyakin da aka sarrafa a ƙasar Sin suna ɗauke da wannan kalmar 'Made in China'

  Tecno phones now carry a thirteen-month warranty. yanzu wayoyin tecno suna da garantin watanni goma sha uku.

  The book carried inspirational stories that he no aware of. akwai labarai masu ƙarfafa gwiwa a cikin littafin da bai ankara da su ba.

  Same sex marriage carries ten years imprisonment in Nigeria. auren jinsi ɗaya yana ɗaukan hukuncin ɗaurin shekaru goma a Nigeria.

  Security job carry alot of risk. aikin tsaro yana tattare da hatsari.

  Rape case carries death penalty in some countries. hukuncin  kisa ne ake yankewa masu fyaɗe a wasu ƙasashen.

  Giving birth unmarried carries a stigma in northern Nigeria. haihuwa ba tare da aure ba abun kunya ne a arewacin Nigeria.

 9. Ci gaba
 10. The professor carried the theory further. farfesan ya faɗaɗa nazariyar.

  She carries envy to its maximum limits. ta kai ƙarken hassada.

  Children begin learning basic mathematics, then carry further in secondary schools. yara suna fara koyon lissafi ne mai sauƙi, sannan daga bisani sai a ƙara faɗaɗa musu lissafin a makarantun sakandare.

  She always carries her story further if she realized people are attentive. a koda yaushe tana ci gaba da bada labari idan ta fahimci mutane suna sauraronta.

 11. Ɗaukan ciki
 12. Thirteen years old girl is able to carry baby. yarinya 'yar shekara goma sha uku zata iya ɗaukan ciki.

  Some women gain weight when carrying baby. wasu matan suna yin ƙiba lokacin da suke da juna biyu.

English to Hausa Words list

A-B-C-D-E-F-G-H-I-J-K-L-M-N-O-P-Q-R-S-T-U-V-W-X-Y-Z

Hausa to English Words list

A-B-C-D-E-F-G-H-I-J-K-L-M-N-O-R-S-T-U-W-Y-Z

Kamus.com.ng is an online/offline English to Hausa And Hausa to English comprehensive bilingual Dictionary (or Kamus in Hausa) containing thousands of British and American English words/phrases and Abbreviations.

The website/app provide definition of any existing English or Hausa word and phrase.

Each words came along with parts of speech.

We included hausa descriptions of complex and ambiguous definitions

We specified British Audio and IPA pronunciation of any English word for those wishing to know how to pronounce a particular word.

We provide English & Hausa bilingual usage sentences, description images, audio pronunciations of all Hausa words, pluralization of Hausa words, and origins of Hausa words derived from Arabic or English.

However this website came along with English to Hausa learning resources designed specifically for native Hausa wishing to learn English as second language.

Scientific words, medical words, geology, geography, biology, anatomy, chemistry, physics, literature, computing, psychology and linguistics words were included and precisely translated to Hausa.

Enjoy your stay here and also contribute to its growth by linking to us or inform others about this website.

The dictionary is frequently updated and it works both online and offline.

If there is any missing word in the dictionary please send us the word and we'll add the word as soon as possible

Aika Zuwa

Whatsapp

© Copyright 2014-2021 Shamsuddeen Inc. all right reserved